Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 10:49:09    
Mai yiyuwa ne 'yan mata za su kamu da hauhuwar jini idan ba su yi cikakken barci ba

cri
Bisa wani binciken da kasar Birtaniya ta yi, idan 'yan mata ba su yi cikakken barci ba, to, yiyuwar kamuwa da hauhuwar jini zata karu gare su.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya suka bayar, masana kimmiya na jami'ar Oric ta kasar Birtaniya sun yi bincike ga ma'aikata 5766 na hukumomi 20 na gwamnati a birnin London domin nazarin huldar da ke tsakanin barci da hauhuwar jini. A cikinsu akwai maza 4199 da mata 1567.

Masana kimmiya sun ce, bisa sakamakon binciken da aka yi, yiyuwar hadarin kamuwa da hauhuwar jini game da 'yan mata da suka yi barci kasa da awo'i 5 ta ninka sau biyu bisa ta 'yan mata da suka yi barci fiye da awo'i 7, amma, wannan babu bambanci game da maza.

Masu binciken sun ce, ko da yake tasirin da karancin barci ya yi wa maza da mata ba iri daya ba ne, amma karancin barci a jere zai yi mugun tasiri sosai ga lafiyarsu.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani kan yin barci cikin awo'i 7 a ko wace rana ya fi amfana wa lafiyar mutane

Kowa ya sani cewa, rashin barci yana kawo wa lafiyar mutane illa. Amma yin barci cikin dogon lokaci bai amfana wa lafiyar mutane ba. Masana ilmin likitanci sun nuna cewa, yin barci cikin awo'i 7 a ko wace rana ya fi amfana wa lafiya.

Shehun malami Li Shunwei, zaunannen wakilin sashen ilmin kwakwalwa na hadadiyyar kungiyar ilmin likitanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, lokacin barci wani muhimmin abin bara ne wajen tabbatar da rashin barci. Idan wani mutum bai iya yin barci cikin awo'i 6 a duk rana gaba daya ba, to, likitoci sun tabbatar da cewa, wannan mutum ya kamu da ciwon rashin barci.

Yin barci cikin dan lokaci kadan zai kawo wa lafiyar mutane illa. Nazarin da aka yi ya nuna cewa, masu fama da rashin barci da yawansu ya kai kashi 80 zuwa 90 cikin dari suna fama da sauran ciwace-ciwace, wadanda ke kunshe da ciwon zuciya da hawan jini da sauran ciwace-ciwace masu tsanani.

Mr. Li ya tsamo sakamakon nazarin da abin ya shafa ya yi nuni da cewa, yin barci cikin dogon lokaci ko kuma cikin dan lokaci kadan suka haddasa ciwon sukari da ciwon zuciya, har ma sun kara wa mutane barazanar mutuwa, yin barci cikin awo'i 7 a ko wace rana ya iya rage wa masu fama da ciwon sukari da ciwon zuciya barazanar mutuwa.

Masanan da abin ya shafa sun nuna cewa, a galibi dai akwai manyan dalilai 3 da suka ba da tasiri kan barci su ne ciwace-ciwace da halin mutane da kuma matsin lambar aiki da dangantakar da ke tsakanin mutane. Ga misali, ciwo ya kan ba da tasiri kan barci, haka kuma, jarrabawa ta kan ta da hankalin dalibai.

Wasu kwararru masu ilmin abinci masu gina jiki sun ba da shawarar cewa, abinci masu yawa sun ba mutane taimako a fannin yin barci. Madara mai zafi da ke kunshe da zuma da dabino da tuffa da dai sauransu dukkansu suka ba da taimako wajen yin barci, haka kuma zaben abinci yadda ya kamata yana iya daga ingancin barci.

A sa'i daya kuma, Mr. Li ya ce, an sami wadannan sakamakon nazari ne bayan da aka yi nazari kan yawancin mutane, ba a iya kawar da cewa, ko da yake su kan yi barci cikin awo'i 4 zuwa 5 a ko wace rana, ko kuma cikin awo'i fiye da 10, wasu mutane suna da lafiya ba.(Musa)