Ran 1 ga wata da safe, a nan Beijing, an kaddamar da shekarar yawon shakatawa ta gasar wasannin Olympic ta kasar Sin ta shekarar 2008.
Malam Shao Qiwei, shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga wannan rana, an kaddamar da shekarar yawon shakatawa ta gasar wasannin Olympic ta kasar Sin ta shekarar 2008 a hukunce. Babban takenta shi ne 'shirya gasar wasannin Olympic a Beijing da kuma saduwa da juna a kasar Sin'. Za a gudanar da jerin tarurukan dandalin mu'amala da harkokin musamman kan yawon shakatawa game da gasar wasannin Olympic. Malam Shao ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi amfani da damar shirya gasar wasannin Olympic wajen samar da siffarta a duniya, wato ita ce wata kasa ta zamani mai dogon tarihi da wayin kai, za ta kuma kyautata matsayin ba da hidima ta fuskar yawon shakatawa.(Tasallah)
|