Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-01 17:18:11    
An yi kasaitaccen biki domin maraba da shekara ta gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Ran 31 ga watan Disamba na shekarar 2007 da dare, a nan Beijing, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya yi kasaitaccen biki mai lakabi haka 'maraba da gasar wasannin Olympic da hannu biyu biyu da kuma nuna wa Beijing fatan alheri' domin maraba da shekarar 2008, wato shekara ta gasar wasannin Olympic. Wakilai fiye da dubu 4 na rukunoni daban daban na Beijing sun taru domin barka da shekara ta gasar wasannin Olympic tare.

A wannan rana misalin da karfe 12 na dare, tare da farin ciki da 'yan kallo suka nuna, Duan Shijie, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin wasanni ta kasar Sin da Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma madam Tang Xiaoquan, shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin nakasassu ta kasar Sin kuma mataimakiyar shugaban gudanarwa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun kaddamar da babban injin ba da haske tare, wanda aka rubuta 'We Are Ready', wato A shirye muke a kansa. Nan da nan kalmomin 'maraba da gasar wasannin Olympic da hannu biyu biyu da kuma nuna wa Beijing fatan alheri' domin maraba da shekarar 2008' sun bullo a gine-ginen da ke kewayen 'yan kallo. 'Yan kallo sun yi murna sosai.

A sa'i daya kuma, wasu nagartattun mutanen kasar Sin da na kasashen waje sun buga kararrawa tare domin yin ikirarin cewa, Beijing ta shiga shekara ta gasar wasannin Olympic a hukunce.(Tasallah)