Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-31 19:15:35    
Kasashen Afirka suna kokarin bunkasa kansu cikin himma

cri
Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa a duk duniya. A shekarar 2007, hankulan karin kasashen Afirka sun juya ga bunkasuwar tattalin arziki da raya kansu.

A shekarar 2007, a karo na farko ne saurin bunkasuwar tattalin arziki da kasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara suka samu ya wuce matsakaicin matsayin duniya. An kiyasta cewa, irin wannan adadi zai kai kashi 6 cikin kashi dari. A watan Mayu, kafada da kafada Kungiyar yin hadin gwiwar tattalin arziki da kula da harkokin bunkasuwa da bankin raya Afirka suka fito da rahoto mai lakabi haka 'hangen nesa da aka yi kan tattalin arziki', inda aka nuna cewa, a cikin kasashen Afirka, wasu 20 kamar su kasashen Kenya da Angola da Nijeriya sun sami saurin bunkasuwar tattalin arziki.

Yawancin manazarta sun yi hasashen cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Afirka ta fi dogara da kyautatuwar tsaron kai a galibin kasashen Afirka. A ran 16 ga watan Oktoba, Kemal Dervis, shugaban hukumar tsara shiri kan bunkasuwa ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya kammala ziyararsa a Afirka ba da jimawa ba, ya nuna cewa,'A cikin dimbin muhimman dalilai, a ganina, kawo karshen rikici a gida da kuma a tsakanin kasashe masu makwabtaka da juna ya zo a gaban kome a fannin neman bunkasuwa.'

Baya ga neman samun kwanciyar hankali, kasashen Afirka sun gano cewa, sun gagara wajen tinkarar kalubalen da raya tattalin arzikin kasashen duniya gu daya ke kawo musu da kansu saboda tattalin arzikinsu na baya sosai a sakamakon wasu dalilan tarihi. Shi ya sa kasashen Afirka suka hada kansu. A shekarar 2007, kungiyoyin shiyya-shiyya na Afirka sun ci gaba da taka muhimmiyar rawa. A matsayin kungiya mafi girma, wadda kuma ta fi ba da tasiri a Afirka, Kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da yadda za a gaggauta raya Afirka gu daya a matsayin babban taken taron koli a shekarar bana. Kazalika kuma, kasashen Afirka sun gano cewa, ya kamata su inganta hadin gwiwa a stakaninsu da sauran nahiyoyi da kungiyoyin kasa da kasa.

Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taba nuna cewa, ya kamata kasashen duniya su yi kokari tare domin taimakawa Afirka da su tabbatar da makasudin bunkasuwa na shekarar 2000 kafin shekarar 2015. Game da wannan, Osita Agbu, wani manazarci a kwalejin nazarin dangantaka a tsakanin kasa da kasa na Nijeriya, ya bayyana cewa,'Kasashen Sin da Japan da Sweden da Australia da Canada su aminai ne ga Afirka. Suna taimakawa kasashen Afirka ta hanyoyin ba da shawara kan fasaha da kuma taimakon kudi.'

Don tabbatar da samun bunkasuwar kasashen duniya tare, a wannan shekara, kasashe da kungiyoyin duniya da abin ya shafa sun ci gaba da kyautata tsarin bai wa Afirka tallafawa, sun kuma karfafa karfin taimako. Tsarin taron dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ba kawai ya daukaka ci gaban Sin da Afirka a fannoni daban daban ba, har ma ya samar da misali ga sauran kasashe da yankuna domin yin mu'amala da hadin gwiwa da Afirka cikin daidaici. Lin Lin, jakadan kasar Sin a kasar Habasha ya ce,'Tsarin taron dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ya sanya sauran kasashe da yankuna su kara mai da hankulansu kan Afirka. Kasashen Turai sun sami sabon ci gaba a fannin raya hulda a tsakaninsu da kasashen Afirka a shekarun baya. Kasashen Kudancin Amurka kuwa sun kira taron koli na farko a tsakaninsu da Aifkra a birnin Abuja, hedkwatar Nijeriya a karshen shekarar bara. Kasar Sin ta fadakar da su bisa kyakkyawar hulda a tsakaninta da kasashen Afirka. Bugu da kari kuma, sauran kasashen duniya su ma za su mai da hankulansu kan Afirka.'

An yi imani da cewa, saboda kokarin da kasashen Afirka suke yi, da kuma taimakon da kasashen duniya suke bayarwa, tabbas ne kasashen Afirka za su sami karin saurin bunkasuwa.

Kamar yadda El Ghassim Wane, darektan sashen kula da harkokin rikici na kungiyar AU ya fada,'Mun san kalubalen da muke fuskanta. Amma mun yi imani da cewa, Afirka wata nahiya ce da ke da babban boyayyen karfi da ba ta taba amfani da shi ba tukuna, yau da gobe za ta bi hanyar bunkasuwa.'(Tasallah)