Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-31 15:54:12    
Hanyar da ke kawo alheri da ke filin ciyayi

cri
Mun sami labari daga wajen sassan kula da ma'aikatan hukuma na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, an ce ya zuwa karshen shekarar 2006, yawan ma'aikatan hukuma 'yan kananan kabilu na duk jihar Tibet ya wuce 62,000, wato ya kai kusan kashi 70 cikin 100 bisa na dukkan ma'aikatan hukuma na jihar, sabo da haka ma'aikatan hukuma 'yan kananan kabilu sun riga sun zama rundunar ginshiki wajen tafiyar da harkokin jihar Tibet.

Jihar Tibet wata jihar kabilu ce mai ikon tafiyar da harkokin kanta wadda yawancin mutanenta'yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu ne. Cikin shekaru da yawa da suka wuce, kwamitin tsakiya na J.K.S. da kwamitin jam'iyya da hukumomin gwamnati na jihar sun gudanar da "dokar zaman kai a shiyyoyin kabilu" cikin nitsuwa, kuma sun mai da muhimmanci sosai wajen tallafa ma'aikatan hukuma 'yan kananan kabilu da yin amfani da su.

Yanzu direktan majalisar wakilan jama'ar jihar, da shugabannin gwamnati da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da kotun koli ta jama'a na jihar dukkansu 'yan kananan kabilu ne. Yawan jami'ai 'yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu da ke bisa matakin lardi sun kai 40 wato sun kai kusan kashi 70 cikin 100 bisa na dukkan jami'an da ke bisa wannan mataki.

A ran 7 ga watan Disamba na shekarar 2007 a nan birnin Beijing, an yi taron tataunawa domin murnar ranar cika shekaru 50 da kaddamar da mujallar kabilu mai suna "kabilun kasar Sin" kuma mai fada a ji a kasar, wadda kuma aka buga bisa kayadadden lokaci.

An fara buga mujallar "kabilun kasar Sin" daga shekarar 1957, yanzu mujallar nan ta samu bunkasuwa har ta zama wata mujallar da ake bugawa cikin harsuna iri 6 wato harshen kabilar Han da Turanci da kuma harsunan kabilun Mongoliya da Uighur da Hazakh da Korea, kuma ta zama wata muhimmiyar kafar yada labarai wadda kundayenta da ake bugawa sun fi yawa, wadda kuma ta fi nuna muhimmanci daga cikin mujallun kabilun kasar Sin da ake bugawa a kasar Sin.

A shekarar 2007 wato shekara ta farko wajen aikin dasa bishiyoyi a muhimman wurare, fadin gandun daji da aka kirkiro a duk jihar Tibet ta kasar Sin ya kai kusan kadada 7,000 a wannan shekara, yawan bishiyoyin da suka rayu kuma ya wuce kashi 80 bisa 100.

Bisa shirin da aka tsayar an ce, za a dasa bishiyoyi a muhimman wurare ciki har da birane da garuruwa da gefunan hanyar jirgin kasa, da filin jirgin sama da wuraren yawon shakatawa, yawan fadinsu ya kai fiye da kadada 47,000, jimlar kudin da aka ware domin aikin ta kai kusan kudin Sin Yuan miliyan 600. Kuma jihar Tibet za ta dauki wannan aiki tamkar mafarin aiki ne domin kara samun babban ci gaba wajen dasa bishiyoyi a duk jihar.(Umaru)