Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-31 15:11:13    
Amincin da ke tsakanin Mr Simon J. Mackinon da birnin Shanghai na kasar Sin

cri

Malam Simon J. Mackinon dan kasar Birtaniya ne. Ma Ximen sunan Sinanci da ya rada wa kansa ne. Yau kusan shekaru 20 ke nan yake zaune a birnin Shanghai na kasar Sin, matarsa ma 'yar birnin Shanghai ce. Gwamnatin birnin Shanghai ta taba ba shi lambobin yabo da dama, musammam ma a kwanakin baya ta lakaba masa sunan mazaunin birnin mai girmamawa.

A karo na farko Malam Ma Ximen ya kawo wa kasar Sin ziyara a shekarar 1979. Amma bai je birnin Shanghai ba, maimakon birnin Shenzhen da ke a kudancin kasar. A wancan lokacin shi saurayi ne mai shekaru 18 da haihuwa. Bayan da ya gama karatunsa daga jami'a a kasar Birtaniya a shekarar 1985, ya zo birnnin Shanghai da ke a gabashin kasar don koyon Sinanci. Da Ma Ximen ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, "kullum birnin Shanghai cibiyar kasuwanci ce a kasar Sin. Wannan shi ne dalilin da ya sa na zabi birnin Shanghai, na koyi Sinanci. Ban da wannan kuma, ina sha'awar tarihin birnin Shanghai na shekarun 1920 ainun."

Bayan saukarsa a birnin Shanghai a shekarar 1985, ya shafe shekaru uku yana koyon Sinanci a Jami'ar birnin Shanghai, da ya gama karatunsa, sai ya kama aikin koyar da Ingilishi a Jami'ar koyon aikin cinikin waje ta Shanghai. A cikin wannan lokaci ne, ya auri wata budurwa 'yar birnin Shanghai, ya zama surukin birnin kwarai da gaske. Bayan da ya yi aikin koyarwarsa a cikin shekaru da dama, sai ya koma kasar Birtaniya ya fara yin aiki a kamfanin sufurin jirgin ruwa na kasar bisa al'adar iyalinsa. Ya sake komowa birnin Shanghai ne a shekarar 1995. Kuma ya zama babban manajan kamfanin P&O na kasar Birtaniya a babban yankin kasar Sin, daga nan ne yake ta zama a birnin Shanghai. Bisa taimakon da ya bayar wajen kara yin ma'amala a tsakanin Shanghai da kasashen waje, gwamnatin birnin ta ba shi lambar yabo.

Yanzu kasar Sin tana kokari sosai wajen raya birnin Shanghai don ya zama cibiyar tattalin arziki da kudi da ciniki da sufuri a duniya, kuma za a yi kokarin raya birnin don ya zama babban birnin duniya na zamani a shekarar 2020. Malam Ma Ximen ya ce, shi da 'yan kasuwa na kasashen waje da yawa dukanninsu suna sa ran alheri ga mokomar ci gaban birnin. Ya ce,

"birnin Shanghai birni ne da baki 'yan kasashen waje ke sha'awarsa kwarai. Idan ka yi fatan more zamanka cikin kuzari, da cin abinci mai dadi da kuma koyon Sinanci, to, ka zo birnin Shanghai kamar yadda ya kamata. Haka kuma idan kana sha'awar fasaha da dakunan nunin kayayyaki, to, ka zo birnin Shanghai kamar yadda ya kamata. Birnin Shanghai ya yi kamar wani fure da ke tohuwa, yana zama wani birni mai girma."

Malam Ma Ximen ya kafa asusun gyara da kiyaye birnin Shanghai, kuma ya zama mataimakin shugaban asusun. Yanzu yana kokari sosai wajen yin harkokin kiyaye tsofaffin gine-gine na birnin. Bisa babban taimakon da ya bayar, gwamnatin birnin Shanghai ya laba masa sunan mazaunin birnin mai girmamawa, wanda ba safai a kan ba baki na kasashen waje ba. Malam Ma Ximen ya ce, "na taka sa'a sosai. Na shafe shekaru 22 ina zama a birnin Shanghai. Iyalinsa sun zama tamkar wani kamfani ne da aka kafa bisa jarin hadin guiwar Britaniya da Sin, dalilin da ya sa haka shi ne domin matata 'yar Shanghai ce, ni kuma surukin birnin ne."

Yanzu Malam Ma Ximen wani masanin ilmin kasar Sin ne. Ya fahimci tarihi da al'adun kasar Sin, yana jin Sinanci kwarai, yana sha'awar cin abincin Sinawa kwarai. Haka kuma yaransa ba ma kawai suna jin Sinanci fiye da shi ba, har ma suna jin karin harshe na Shanghai. Ana ganin cewa, nan gaba za a kara dankon aminci a tsakanin iyalin Ma Ximen da birnin Shanghai. (Halilu)