A kwanan baya, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya sanar da cewa, zai shirya kasaitaccen biki a nan Beijing a ran 31 ga watan Disamba da dare domin maraba da gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma nuna wa Beijing fatan alheri, inda tare da mazaunan Beijing da dukkan jama'ar Sin zai yi maraba da sabuwar shekara da kuma maraba da kwana na farko na shekarar gasar wasannin Olympic ta Beijing.
Bisa shirin da aka tsara, an ce, da zarar karfe 12 da daddare na ran 31 ga watan Disamba na shekarar 2007, sai wasu shahararrun mutane na kasar Sin za su buga kararrawa domin maraba da sabuwar shekara tare. Wannan ya nuna cewa, Beijing ta shiga shekara ta gasar wasannin Olympic a hukunce.(Tasallah)
|