Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-29 19:00:21    
Shugabannin kasashen Sin da Japan sun samu ra'ayi daya a dukkan fannoni a cikin shawarwarinsu, in ji firayin minista Wen Jiabao na Sin

cri
Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a yau 29 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ziyarar da takwaransa na kasar Japan Yasuo Fukuda ke yi a kasar Sin ta samu nasara, shugabannin kasashen Sin da Japan sun samu ra'ayi daya a dukkan fannoni da ke da nasaba da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A lokacin da Mr. Wen Jiabao da Mr. Fukuda suke yin kumallo tare da kungiyoyin sada zumunci na jama'a na kasashen Sin da Japan suka shirya, ya ce, an samu sakamako sosai a gun shawarwarin da aka yi a jiya ranar 28 ga wata. Gaba daya bangarorin biyu suka bayyana cewa, za a kara kyautata tsarin tattaunawa a tsakanin manyan shugabannin Sin da Japan a fannin tattalin arziki, ta yadda za a karfafa hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.

Mr. Fukuda ya bayyana cewa, shekara mai zuwa shekara ce ta cikon shekaru 30 da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta a tsakanin Japan da Sin, yana fatan shekarar 2008 za ta zama shekarar da aka fi samun bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Japan da Sin a tarihi. (Bilkisu)