Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-28 19:08:43    
Kasashen Sin da Japan sun cimma matsaya guda kan yadda za a kara inganta dangantakar dake tsakaninsu

cri

Yau Jumma'a, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Japan Mr. Fukuda yasuo, wanda yake yin ziyara a nan kasar Sin, inda gaba dayansu suka lashi takwabin kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Bayan shawarwarin Mr. Wen Jiabao ya fada wa manema labaru na gida da na waje, cewa nasarar da aka samu a gun shawarwarin ta sa shi ganin zuwan kyakkyawan yanayin bazara a zahiri. Sa'annan ya furta cewa: " Na taba kai wani rangadin narke kankara cikin nasara a kasar Japan a watan Afrulu na shekarar da muke ciki. Lallai ban manta ba, an yi ruwan sama lokadin da na isa Tokyo. Sai na ce ' kyakkyawan ruwan sama na alamanta kyakkyawan yanayi; Ga shi yau dai, ana kankara yayin da firaminista Fukuda ke yin ziyara a kasar Sin. Bari in sake tsamo wata magana cewa: 'Kyakkyawar kankara na alamanta shekara mai albarka'.

Kafin Mr. Fukuda ya taso daga Japan zuwa nan kasar Sin domin yin ziyara, ya taba fada wa manema labaru na kasar Sin cew: " Dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan ta rigaya ta shiga cikin kyakkyawan yanayin bazara".

Firaministan Wen Jiabao ya bayyana wa kafofin yada labarai na gida da na waje wasu jerin sakamakon da aka samu a gun shawarwarin, inda ya fadi cewa: kasashen biyu sun tsaida kudurin ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba kamar yadda ya kamata; Sa'annan su kara yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, musamman ma a fannin kiyaye muhalli, da yin tsimin makamashi, da harkokin kudi, da kuma na kimiyya da fasaha na zamani da dai sauran fannoni. Kazalika, bangarorin biyu za su gudanar da bikin tunawa da zagayowar ranar cika shekaru 30 da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta tsakanin Sin da Japan yayin da suke kara yin tuntubar juna a fannin tsaro da zaman lafiyar siyasa da dai sauran makamantansu.

An labarta cewa, a gun shawarwarin, Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, kiyayewa da kuma inganta kyakkyawar dangantakar makwabtaka tsakanin kasashen Sin da Japan, wata hanya ce daya tak da bangarorin biyu suka zaba domin hakan ya dace da babbar moriyar jama'ar kasashen biyu da kuma amfana wa zaman lafiya da bunkasuwa na arewa maso gabashin Asiya har da duk kasashen Asiya.

A yayin da firaminista Fukuda yake tabo magana kan dangantakar dake tsakanin kasashen Japan da Sin, ya furta cewa " A zahiri dai, ya kasance da wasu matsaloli tsakanin kasashen biyu. Amma wajibi ne a yi kokarin daidaita su ta hangen nesa, wato ke nan kasashen biyu su Japan da Sin su kara samun fahimtar juna da amince wa juna. Hakan zai iya haifar da kyakkyawan makoma ga kasashen biyu da kuma kara taka muhimmiyar rawa ga gamayyar kasa da kasa'.

A gun shawarwarin, firaminista Wen Jiabao ya bada shawarar cewa, ya kamata shugabannin kasashen Sin da Japan su kai juna ziyara da kuma yin shawarwari tsakanin bangarori da dama daidai kamar yadda suka yi a da. Daga bisani, ya furta cewa : ' Ci gaba da yin musanye-musanye tsakanin manyan jami'ai na kasashen biyu, ya kasance tamkar karfin ingizawa na ingantakawa da kuma kyautata dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. A yanayin bazara na sheara mai zuwa, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai ziyara a kasar Japan, wadda take da muhimmiyar ma'ana '.

Jama'a masu sauraro, batun Taiwan, wani muhimmin batu ne dake shafar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan. Game da wannan dai, firaminista Fukuda ya bayyana ra'ayinsa cewa : gwamnatin Japan ba ta taba canza matsayinta kan batun Taiwan ba, kamar yadda aka bayyana shi cikin hadaddiyar sanarwar hadin gwiwa ta kasashen biyu. Ko kusa ba za mu nuna goyon baya ga yunkurin kirkiro Sin biyu ko Sin daya Taiwan daya ba ; haka kuma mun yi watsi da shirin hukumar Taiwan na kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a don neman shiga cikin Majalisar Dinkin Duniya. (Sani Wang)