" An rigaya an kammala akasarin muhimman ayyukan share fagen taron wasannin Olympics na Beijing daidai bisa shirin da aka tsara", in ji Mr. Liu Jinmin, mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing a gun wani taron ganawa da manema labaru da aka gudanar kwanan baya ba da dadewa ba a nan birnin Beijing,inda ya kuma fadi cewa, hakan ya aza tubali mai inganci ga gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008 lami-lafiya.
Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, kwanaki kasa da 300 ke nan da suka rage a gudanar da wannan gagarumin taron wasanni. Shekaru sama da 6 da suka shige bayan da gwamnatin birnin Beijing ta cimma nasarar daukar bakuncin taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008, ana gudanar da ayyukan share fage iri daban-daban kamar yadda ya kamata duk bisa goyon baya daga gwamnatin kasar Sin da jama'arta. A gun taron ganawa da manema labaru da aka gudanar a albarkacin babban taron wakilan duk kasa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a karo na 17, Mr. Liu Jinmin ya bayyana cewa: " Yanzu, an rigaya an kammala muhimman ayyuka iri daban-daban na share fagen taron wasannin Olympics daidai cikin lokaci, wato ke nan an kammala gina filaye da dakuna 27 na yin gasanni daga cikin 37, wadanda za a yi amfani da su domin taron wasannin Olympics na Beijing; Ban da wannan kuma an riga an tabbatar da shirye-shiryen gudanar da bikin taron wasannin Olympics na Beijing da kuma bikin rufe shi; Kazalika,yanzu ana gaggauta yin ayyukan shirin mika wutar yula mai tsari ta wannan kasaitaccen taron wasannin Olympics".
Daga bisani, Mr. Liu Jinmin ya bayyana cewa, ana gudanar da harkokin yin odar tikitocin taron wasannin da kuma na sayar da su lami-lafiya; kuma ana tabbatar da takardun odar sayen tikitoci da aka samu daga ketare; Kazalika, ana horar da masu aikin sa kai na taron wasannin Olympics kamar yadda ya kamata, wato ke nan yawan mutanen da suka yi rajista ya riga ya dara 670,000. Ban da wadannan kuma, ana gudanar da ayyukan share fagen taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing a shekarar 2008 a lokaci guda yayin da ake gina filaye da dakunan wasanni maras shinge.
Cikin shekaru fiye da shida da suka wuce, an samu kyautatuwar muhallin halittu da kuma muhimman gine-gine na sufuri na birnin Beijing a bayyane.
Aminai masu sauraro, idan ba ku manta ba, a duk tsawon lokacin da gwamnatin birnin Beijing take rokon samun iznin gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing, ta fito da shirin " gudanar da taron wasannin Olympics cikin kyakkyawan yanayi", wato ke nan ta alkawarta rage tasiri maras kyau da akan samu ga muhallin birnin sakamakon ayyukan share fagen taron wasannin da ake yi, da kuma samun dauwamammen ci gaban sha'anin kiyaye muhalli na birnin. Mr. Liu Jinmin ya yi nuni da cewa: " A duk tsawon lokacin da ake share fagen taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008, muna namijin kokari wajen cika alkawaran da muka dauka a wadannan fannoni biyu har mun samu sakamako mai armashi. Nan gaba, za mu ci gaba da yin kokari wajen cika alkawarin kirkiro wani kyakkyawan yanayi domin taron wasannin Olympics na shekara mai kamawa".
Aminai 'yan Afrika, aikin tsaro, wani muhimmin aiki ne daga cikin ayyuka mafi muhimmanci na share fagen taron wasannin Olympics da akan yi har kullum. Game da wannan batu, Mr. Liu Jinmin ya kara bada hasken cewa: " Bisa bukatun kwamitin wasannin Olympics na duniya, mun kaddamar da wani cikakken shirin samar da tsaro ga taron wasannin Olympics, wato ke nan mun tsara wani ingantaccen shirin bada umurni ga yin tsaro na matakin kasa ga taron wasannin Olympics; A sa'I daya kuma, sassan da abin ya shafa sun yi nazarin fasahohi da kuma darussan da aka samu a fannin tsaro daga tarurrukan wasannin Olympics da aka gudanar a da, har sun dauki wasu jerin matakan fasahohi na zamani da akan dauka a duniya".
A gun taron manema labaru da aka shirya, Mr. Liu Jinmin mai cike da imanin cewa, ta taron wasannin Olympics na Beijing, ko shakka babu birnin Beijing zai iya kara samun farin jini a sauran kasashen duniya da kuma bunkasuwar tattalin arziki. ( Sani Wang )
|