Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-27 18:01:41    
Kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia

cri

Kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin tana birnin Yinchuan, hedkwatar jihar, kuma an kafa ta a shekara ta 1985 domin horar da manya maza da mata masu aikin koyar da addinin Musulunci.

Shugaban kwalejin Su Yang ya gaya mini cewa, yanzu akwai malamai 51 da kuma dalibai 325 a cikin kwalejin, kuma muhimman darusan da ake koyarwa su ne harshen Larabci, da Alkur'ani, da labarin wali Muhamoud, da dokokin addinin Musulunci, da harshen Sinanci, da Turanci, da dai sauransu. Ya zuwa yanzu dalibai kusan 1500 sun riga sun gama karatunsu daga kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia, kuma suna gudanar da ayyukansu a fannoni daban daban da ke da nasaba da addinin Musulunci da kuma harshen Larabci.

Sabo da kwalejin tana koyar da ilmin addinin Musulunci, shi ya sa ta jawo hankulan kasashen Larabawa sosai. Lokacin da aka kafa ta, bankin raya kasashen musulunci na duniya ya samar da kudin taimako, haka kuma ya zuwa yanzu baki dubbai da suka zo daga kasashe fiye da 100 sun zo kwalejin don yin ziyara, ciki har da sarkin kasar Saudi Arabia da sarkin kasar Malaysia, da yariman daular hadaddun sarakunan Larabawa da dai sauransu. Sabo da haka, shugaba Su Yang na kwalejin ya bayyana cewa, kwalejin wata shaida ce wajen zumuncin da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa da ke shiyyar gabas ta tsakiya, haka kuma wata gada ce wajen hada Sin da kasashen Musulunci tare. Shi ya sa dole ne zai bayar da gudummowarsa wajen raya sha'anin addinin Musulunci a kasar Sin, da kara zumunci da cudanya tsakanin kasarmu da kasashe daban daban na Musulunci, da kuma sa kaimi ga aikin bude kofa ga kasashen waje da jihar Ningxia ke yi.(Kande Gao)