Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-27 17:58:39    
Gidan marayu musulmai na farko na jihar Ningxia

cri

An kafa gidan marayu musulmai na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin a ran 20 ga watan Yuni na shekarar nan da muke ciki, wanda yake gundumar Xingjing da ke karkashin jagorancin birnin Yinchuan, hedkwatar jihar, wannan shi ne gidan marayu musulmai na farko na jihar, kuma fadinsa ya kai murabba'in mita 2100, inda ake cikin shirin karbar marayu 300.

Abdu Al Halik, shugaban kungiyar jin kai ta musulunci ta jihar Ningxia ya bayyana cewa, kwamitin kula da musulmai na kasashen Asiya na kungiyar jin kai ta musulunci ta kasa da kasa ta kasar Kuwait shi ne ya samar da kudin Sin wato Yuan miliyan 1.8 don hadin gwiwa tare da kungiyar jin kai ta musulunci ta Ningxia wajen kafa wannan gidan marayu. Kuma ya gaya mini cewa, dalilin da ya sa ya kafa gidan marayu shi ne sabo da shi wani maraya ne, a lokacin yarantakarsa ya sha wahala sosai, shi ya sa bayan da ya girma, yana da aniyar kafa wani gidan marayu domin su iya samun kyakkyawar kulawa da kuma damar samun ilmi.

Duan Juan wata malama ce ta gidan marayu musulmai na jihar Ningxia, lokacin da na gan ta, na ji mamaki sosai, ita wata budurwa ce wadda shekarunta ya kai 22 da haihuwa kawai. A shekarar da ta gabata, ta gama karatunta daga sashen harshen Sinanci na jami'ar Ningxia, kuma ta gaya mini cewa, dalilin da ya sa ta zo gidan marayu shi ne sabo da ta nuna tausayi sosai ga wadannan yara, kuma kamar yadda waliyai su kan ce, idan an kula da marayu, to zai iya yin zama tare da Allah har abada. Ban da wannan kuma ta bayyana cewa, lokacin da wadannan yara suke gidajensu, kakaninsu suna iya samar da isasshen abinci gare su, amma ba su iya ba da tabbaci gare su wajen samun ilmi. Bayan da suka shiga gidan marayu, an fi dora muhimmanci kan ba da ilmi domin su iya zama kwararru a nan gaba.(Kande Gao)