Wata daliba ta yi abin kirki:Wata daliba a Jamui'ar Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin ta sami lambar girmmawa sabo da ba da jini ga wata mace mai ciki dake bakin mutuwa.Sunan daliba shi ne Mao Chenbing daga birnin Hangzhou na lardin Zhejiang tana da jinin samfurin AB wanda daga mutane dubu goma ke iya samu dayan dake da irin wannan jini cikin mutanen Sin.A wata jiya ranar lahadi da ta yi hira da abokanta ta yanar internet ta sami labari cewa wata mace tana bakin mutuwa tana bukatar jini sanfurin AB cikin gaggawa.Bisa labarin da aka bayar,an ce wannan mace mai bukatar jini wata mace ce ta karamar kabilar Dong dake lardin Guizhou wadda ta yi nisa daga wannan daliba.
Wannan daliba,yarinya ce daga wani gidan matalauci a kauye.Har zuwa wannnan lokaci ta biya kudin makaranta rabi kawai na wannan semester sabo da ba ta da isashen kudi.Duk da haka ta yi aron kudi daga 'yan ajinta domin saye tikitin jirgin kasa da na jirgin sama,da farko ta dau jirgin kasa daga Hangzhou zuwa Shanghai, sannan ta dau jirgin sama daga Shanghai zuwa Guizhou.Ta sauka filin jiragen sama na Guizhou da karfe tara da rabi na dare,iyalin mata mai ciki ya yi mata maraba da hannu bibbiyu.Da suka isa asibitin bayan da daliba ta sha wahala sosai saboda hanyar tafiya ta yi tsawo kuma hanyar mota mai galan suka bi,sai nan da nan ta ba da jini ga matar.Bayan ta bayar da jini har ta sume saboda ta gaji kwarai da gaske.Da ta farka tana so ta ci gaba da ba da karin jini ga matar mai ciki.Amma doktar bai yarda ba.Wannan daliba ta ce "na jin kunya da na ga wannan mata mai ciki tana fama da mutuwa tana bukatar jini,da ba na iya baiwa mata taimako."Daliban nan ta yi wannan magana ne yayin da ta yi hira da dan jariar "Oriental Morning Post" ta kasar Sin. Bayan da ta dawo jami'ar ba ta gaya wa 'yan makaranta kome ba kan abin kirki da ta yi.Har zuwa ranar talata lokacin da shugaban gundumar Liping inda asibitin da mata mai ciki ke kwance ya iso jami'ar,labarinta ya fito.A wannan rana Jami'ar da dalibar ke karatu a ciki ta ba ta lambar girmamawa domin yaba aikin kirkin da ta yi.Mace mai ciki ma ta warke sosai.
Wani karamin yaro ya yi tafiya a mota ba tare da sayen tikiti ba.A ranar lahadi wani karamin yaro mai shekaru uku da haihuwa ya zagaya birnin Nanjing,babban birni na lardin Jiangsu na kasar Sin ya koma gidansa lami lafiya.Karamin yaron ya yi tafiya cikin mota ta rabin rana,daga baya ya yi kuka sabo da yana so ganin iyayensa.Direban motar bus Mr Fu yana tsammanin watakila yaron ya fito ne da iyalinsa,daga baya ya bace.sai ya nemi taimako daga 'yan sanda.ku sani karamin yaron bai iya magana sosai ba,shi ya sa da wuyan a kai shi gida.Duk da haka 'yan sanda da ma'aikatan bus sun yi kokari ta hanyoyi daban daban,daga bisani sun samu nasarar kai yaron gidan.
Wani tsoho ya kashe aurensa.Wani tsoho mai suna Li ya yi rabuwa da matarsa a lardin Taiwan na kasar Sin bayan da ta sha azaba cikin shekaru kimanin arba'in bisa goyon 'yan iyalinsa.Bayan da tsohon ya yi aure a shekara ta 1969,ba da dadewa ba ta fara sha azaba.Matarsa ta kan zage shi cikin jama'a, ta kuma tilasta shi da ya yi barci waje da gida.Kafin shekaru biyu ta soka shi a baya da almakashi,ta kuma duka 'ya'yuansa na balagai.Kotun ta yanke hukuncin kashe aure saboda ta yi ayyuka ba daidai ba ne.
Wani mutumin ya kashe mankudan kudade domin matar aure. Wani saurayi mai kudi daga birnin Shanghai ya kashe kudin Sin RMB Yuan miliyan daya da digo daya,wato dalar Amurka dubu 146 duk domin hayar wasu kwararru da su taimake shi wajen samun buduwar aure,wannan abu ya faru ne a birnin Nanjing na kasar Sin. Bisa labarin da aka samu,an ce an haifi wannan saurayi ne a shekara ta 1981,yana da kudin Sin Yuan miliyan hamsin.Ya zo ne daga wani kauye a lardin Shandong na kasar Sin ya samu kudinsa ne a kasuwar hada hadar kudade.Yana so ya samu wata matar aure daga birnin Nanjing da shekarunta bai wuce ashirin da shida ba.Da samun labari,budurwoyi sama da dari da ashirin suna so su aure shi ciki har da 'yan jami'ar.
Fasahar zamani ta kalubalanci barayi.A ranar jumma'a wani dan sanda a titi ya ga wani mutum ba ya iya amfani da wayar salula ba,sai ya yi shakkunsa,daga baya an gano shi da sauran abokansu biyu dukkan barayi ne.'Yan sanda na tashar jiragen kasa ta Nanchang ta lardin Jianxi na kasar Sin sun iske samari guda uku da suka yi aiki ba daidai ba ne yayin da suka ga wani daga cikinsu bai iya amfani da wayar salula ba.Da ganin haka 'yan sandan sun kirawo su sun yi musu tambayoyi da binciken kayayyakin da suka dauke da su,daga baya suka gano wasu wayoyin salula da naurorin MP4 a cikin kayayyakin da suka tanada.samarin ma sun amshi laifinsu su barayi ne.
---Kare ya zama aminin balbela. Wani kare a birnin Nanjing na lardin Jiangsu na kasar Sin ya kulla aminci da balbela wadda ta ji rauni.Karen ya yi mata gadi a daukacin dare har zuwa kashegari. Wata mazauniyar birnin Nanjing da ta ji karenta ta yi haushi a safiyar ranar lahadi ta gano wata balbela ta shiga tarkon da aka girka ta kuma ji rauni.Da ganin haka ta ceci balbera ta yi mata jinyya.Duk lokacin da take yin wannan aiki,karenta ya zauna kusa,ya yi fushi kwarari idan wani ya kusanci su.Matar Su ta ce idan karen bai kare balbela ba,sauran dabbobi za su iya cinye ta.Shi ya sa karen ya kare ta.Daga baya balbela ta samu sauki da yamma ta tashi sama ta yi tafiyar abinta.(Ali)
|