Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 16:03:11    
Firayin ministan kasar Japan yana fatan za a kai huldar da ke tsakanin Japan da kasar Sin a wani sabon mataki

cri

Tun daga ran 27 ga wata, firayin ministan kasar Japan Fukuda Yasuo zai kawo wa kasar Sin ziyara. Sabo da haka, a ran 25 ga wata da dare, Mr. Fukuda Yasuo ya karbi ziyarar da manema labaru na kasar Sin da ke zaune a kasar Japan suka kai masa, inda ya bayyana cewa, yana fatan za a iya kara raya huldar da ke tsakanin kasar Japan da kasar Sin, kuma shekara mai zuwa za ta iya zama shekarar da za a samu bunkasuwar huldar da ke tsakanin Japan da Sin cikin sauri sosai.

Mr. Fukuda Yasuo ya ce, yana farin ciki sosai domin zai kawo wa kasar Sin ziyara lokacin da ake murnar cikon shekaru 35 da kafuwar huldar diplomasiyya a tsakanin Japan da Sin. Lokacin da yake ziyara a nan kasar Sin, zai gana da shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao, inda za su yi musayar hakikanan ra'ayoyi kan yadda za a kafa huldar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu da kuma yadda kasashen biyu za su iya bayar da gudummowarsu ga kasashen biyu da yankin da suke ciki ta hanyar yin hadin guiwa a tsakaninsu.

Mr. Fukuda Yasuo ya ce, kyakkyawar huldar da ke kasancewa a tsakanin kasashen biyu ba ma kawai za ta amfana wa kasashen biyu ba, har ma tana da muhimmanci sosai ga zaman lafiya da bunkasuwa na yankin Asiya da tekun Pacific.

A waje daya kuma, Mr. Fukuda Yasuo ya bayyana cewa, kasar Japan za ta daidaita batun tarihi cikin halin kamilanci, kuma za ta ci gaba da kasancewa a nan duniya tamkar wata kasa mai kiyaye zaman lafiya. Bisa wadannan ka'idoji ne kasar Japan za ta raya hulda a tsakaninta da kasar Sin da ke fuskantar nan gaba da raya yin shawarwari da mu'amala a tsakaninsu a fannoni daban-dabam kuma a matakai daban-dabam, musamman kara yin musanye-musanye a tsakanin matasan kasashen biyu wadanda suke da nauyin neman bunkasuwa a nan gaba bisa wuyansu. Shekara mai zuwa shekara ce ta cikon shekaru 30 da aka kulla "yarjejeniyar sada zumunta da zaman lafiya a tsakanin Japan da Sin". Sabo da haka, kasashen biyu dukkansu sun yarda da cewa, shekara mai zuwa "shekara ce ta yin musanye-musanye cikin lumana a tsakanin matasan kasashen biyu".

Kan batun yadda za a kafa huldar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen Japan da Sin, Mr. Fukuda Yasuo ya ce, bayan da tsohon firayin minista Abe Shinzo na kasar Japan ya kawo wa kasar Sin ziyara a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, da ziyarar da firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin ya kai wa kasar Japan ziyara a watan Afrilu na shekarar da muke ciki, huldar da ke tsakanin kasashen Japan da Sin tana samun cigaba kamar yadda ya kamata. Domin huldar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen biyu za ta iya samun hakikanan abubuwa, shugabannin kasashen biyu suka ci gaba da kai wa juna ziyara da kafa huldar sada zumunta a tsakaninsu yana da muhimmanci sosai. Mr. Fukuda Yasuo ya bayyana cewa, shi da shugabannin kasar Sin za su tattauna kan makomar huldar da ke tsakanin kasashen Japan da Sin da yadda za a hako albarkatun dake karkashin tekun gabas da batun nukiliya na kasar Koriya ta arewa da batun sauyin yanayin duniya da sauran batutuwan da suke fuskanta tare. Haka kuma, Mr. Fukuda ya kara da cewa, cigaban tattalin arzikin kasar Sin wata kyakkyawar dama ce ga kasar Japan da sauran kasashen duniya, kuma yana da muhimmaci sosai ga cigaban tattalin arzikin kasar Japan.

Bugu da kari kuma, lokacin da yake zantawa kan batutuwa yadda kasashen biyu za su yi hadin guiwa a fannonin kiyaye muhalli da makamashi, Mr. Fukuda ya ce, kiyaye muhalli da makamashi muhimman fannoni ne da kasashen biyu suke yin hadin guiwa. Bisa kokarin da gwamnati da kungiyoyin jama'a suke bayar tare da bangaren kasar Sin, kasar Japan za ta yi amfani da fasahohi da ilmi da take mallaka wajen kyautata fasahohin yin amfani da kwal a tashoshin samar da wutar lantarki da karfin kwal da rigakafin gurbata ruwa da nuna goyon bayan kokarin raya tattalin arzikin bola jari.