Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 11:02:20    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(20/12-26/12)

cri
Ran 22 ga wata, a birnin Changsha da ke kudancin kasar Sin, an rufe gasar neman zama zakara ta wasan kwallon tebur ta kasa da kasa ta shekarar 2007. Dan wasa Wang Hao da 'yar wasa Wang Nan sun zama zakaru a cikin gasa ta tsakanin namji da namiji da kuma gasa ta tsakanin mace da mace. A cikin gasar karshe ta tsakanin namiji da namiji, Wang Hao ya lashe abokin kungiyarsa Ma Lin da ci 4 da 2. Sa'an nan kuma, Wang Nan ta lashe abokiyar kungiyarta Li Xiaoxia da ci 4 da 3 a cikin gasar karshe ta tsakanin mace da mace.

A ran 21 ga wata, a birnin Zurich na kasar Switzerland, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA ta gabatar da sabon jerin kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata na kasa da kasa, wanda shi ne jerin kungiyoyin kasa da kasa na karshe a shekarar 2007. Kungiyar kasar Sin ta zama ta 13, wannan ne karo na farko da kungiyar kasar Sinba ta shiga kungiyoyi 10 da ke kan gaba a cikin irin wannan jerin kungiyoyin kasashe na karshe na shekara-shekara ba. Kungiyoyin kasashen Jamus da Amurka da Sweden sun zama na farko da na biyu da na uku.

Ran 18 ga wata, a birnin Zurich na kasar Switzerland, kungiyar FIFA ta kaddamar da sakamakon zaben 'yan wasa mafiya nagarta na kasa da kasa a shekarar 2007. Shahararren dan wasa Kaka da 'yar wasa Marta na kasar Brazil sun sami lambobin yabo a matsayin 'yan wasa mafiya nagarta a duniya.

Ran 24 ga wata, a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin ta gabatar da sabuwar takardar sunayen 'yan wasan kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin da za su sami aikin horaswa tare. Wannan takarda ta tanadi mashahurran 'yan wasa Feng Kun da Zhao Ruirui, wadanda suka dade suna fama da rauni. Ran 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa, wadannan 'yan wasa da ke cikin wannan takardar sunaye za su taru a birnin Zhangzhou da ke kudancin kasar Sin, za su kaddamar da aikin horaswa na share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing a karkashin shugabancin Chen Zhonghe, malamin horaswa.

Ran 17 ga wata, a babban zaurenta a birnin London na kasar Birtaniya, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tennis ta kasa da kasa wato ITF ya sanar da bai wa dan wasa Roger Federer na kasar Switzerland da 'yar wasa Justine Henin ta kasar Belgium lambobin yabo na zakarun duniya na shekarar 2007.

Ran 21 ga wata, a birnin Madrid, tsohon shugaban kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa wato IOC Mr. Juan Antonio Samaranch mai shekaru 87 da haihuwa ya koma gida daga asibiti. Ran 19 ga wata, an kai masa wani asibiti a Madrid domin ya yi suma ba zato ba tsammani, an kuma yi masa jinya a asibitin. A lokacin da ya shiga asibitin, ya nuna alamar hawan jini a bayyane. Tun daga shekarar 1980 zuwa shekarar 2001, Mr. Samaranch ya yi shekaru 21 yana kan kujerar shugaban kwamitin IOC, yanzu an mayar da shi a matsayin shugaba mai girmamawa na kwamitin IOC.(Tasallah)