Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-25 16:53:54    
Kasar Sin tana gudanar da aikin kafa dokokin shari'a, domin kare kadarorin gwamnati

cri

A ran 23 ga wata, shirin dokar kare kadarorin gwamnati ta kasar Sin, wanda aka tattauna cikin shekaru 14 da suka gabata, ta shiga cikin ajandar dokokin shari'a. Dalilin da ya sa aka fitar da wannan doka shi ne, domin kare kadarorin gwamnati, da hana bacewar kadarorin gwamnatin kasar Sin. Shirin dokar kare kadarorin gwamnati ba kawai zai daidaita matsaloli da ake fuskanta a halin yanzu kawai ba, har ma zai mai da hankali sosai kan abubuwa da za su faru a nan gaba.

Mataimakin darektan hukumar tattalin arziki da kudi na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr Shi Guangsheng ya bayyana cewa, babbar matsala ta bacewar kadarorin gwamnati, da kuma fitowar dokar ikon mallakar dukiyoyi, sun haddasa babbar bukata domin kafa dokar kare kadarorin gwamnatin kasar Sin. Game da haka, ya ce,

'A yayin da ake yin gyare gyare kan tsarin kamfanonin gwamnati, a kan samu bacewar kadarorin gwamnati, jama'a da rukunoni daban daban sun mai da hankali sosai kan haka. Wannan ya bukaci a kafa dokar musamman, da kuma kyautata tsarin da abin ya shafa, domin kare kadarorin gwamnati yadda ya kamata, ta yadda za a iya bunkasa tattalin arzikin gwamnati.'

A cikin shirin dokar kare kadarorin gwamnati, aka fi mai da hankali kan yadda za a kafa tsarin sa ido da kula da kadarorin gwamnati. Game da haka, shirin dokar ya tanadi cewa, kasar Sin za ta kafa tsarin sa ido da kula da kadarorin gwamnati a matsayin tattalin arziki iri na kasuwanci da kuma na gurguzu, majalisar gudanarwa ta kasar Sin da kuma gwamnatoci na wurare daban daban ba su tsoma baki cikin ayyukan harkokin kamfanoni ba. Game da haka, Mr Shi Guangsheng ya ce,

'Ta haka ne, za mu iya daidata matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, dangane da tabbatar da ikon kadarorin gwamnati da moriyarsu, haka kuma za a share fage ga aikin da za a gudana a nan gaba, domin kara kyautata wannan tsarin kare kadarorin gwamnati.'

Wani abu daban da ke jawo hankulan jama shi ne, yadda za a hana bacewar kadarorin gwamnati daga tsari. Game da haka, shirin dokar kare kadarorin gwamnati ya kara karfafa aikin sa ido daga kwamitocin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin daban daban, da gwamnatoci na wurare daban daban, da hukumomin bincike. Shirin dokar kare kadarorin gwamnati kuma ya tanadi ajandar nada shugabannin kamfanonin gwamnati, da yadda za a bincike su, haka kuma shirin dokar ya bayar da ikon sa ido ga ma'aikatan kamfanonin gwamnati. Game da haka, Mr Shi ya bayyana cewa,

'Abubuwan da aka tanada cikin shirin dokar kare kadarorin gwamnati, sun kafa wata hanyar da ake bi, domin kare kadarorin gwamnati, da hana bacewarsu.'

A wannan makon da muke ciki, mambobin kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su dudduba shirin dokar kare kadarorin gwamnati, domin kara kyautata shi.(Danladi)