Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-25 15:42:43    
Kolejin Confucius ya ba da sauki ga kasashen ketare wajen koyon Sinanci

cri

Mataimakin ministan ba da ilmi na kasar Sin Mr. Zhang Xinsheng ya ce:

"Kolejin Confucius kan rediyon tana da fifikon da ba a iya maye gurbi ba, tana iya biyan bukatun jama'a daga kasashe daban daban na duniya wajen koyon Sinanci. Da farko, rediyon kasar Sin na da fasahohi da yawa a fannin koyar da Sinanci. Na biyu, kolejin confucius kan rediyon ya hada da abin musamman na aikin koyarwa ta hanyar internet."

A hakika dai, tun daga shekarar 2004 kasar Sin ta soma kafa hukumomin koyar da harshen Sinanci ga jama'ar kasashen waje a wurare daban daban na duniya. Ya zuwa yanzu, ta riga ta kafa kolejin Confucius sama da 200 a kasashe da shiyyyoyi fiye da 60. Amma, bisa karuwar yin cudanya a tsakanin Sin da kasashe daban daban na duniya, kolejin Confucius na kasancewa da matsalar rashin isassun malama. A cikin wannan halin da ake ciki, an kafa wannan kolejin Confucius kan rediyon.

direktar ofishin kungiyar shugabanci na kasar Sin wajen yada harshen Sinanci tsakanin kasa da kasa madam Xu Lin ta taya murnar kafa kolejin Confucius ta hanyar rediyo, ta bayyana cewa:

"Ba shakka Kolejin Confucius ta hanyar rediyon ya taka mihimmiyar rawa fiye da yadda muka yi tsamani."

Yanzu da akwai kulob din masu sauraron rediyon kasar Sin da yawansu ya kai fiye da 3,000 wadanda ke kasance ko'ina na nahiyoyi 5 na duniya. Kolejin Conficius ta rediyo za ta zabi wasu daga cikinsu don samar da musu da shirye-shirye na musamman. Yanzu yawan irin wuraren da aka kebe ya kai 10, daga cikinsu har da dakin ba da darussa ta hanyar watsa labari da ke birnin Nairobi na kasar Kenya, da na hadaddiyar kungiyar sada zumunci tsakanin Japan da Sin da ke wata gundumar kasar Japan.

Shugaban gidan rediyon kasar Sin Mr. Wang Gengnian ya ce:

"Kolejin Confucius kan rediyon zai yi kokari domin kafa gada a tsakanin jama'ar Sin da na kasashen ketare wajen yin cudanyar al'adu ta harsuna, kuma zai ba da taimakonsa a fannin tabbatar da bunkasuwar al'adu na duniya ta hanyoyi da dama, da kuma shimfida yanayi mai jituwa a duniya."

Mun yi imani cewa, abokanmu na kasashen ketare da yawa za su zabi kolejin Confucius kan rediyon a matsayin abokinsu wajen koyon harshen Sinanci. (Bilkisu)


1 2