Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-25 15:17:15    
Mazaunan kasar Sin suna kokari sosai wajen sayen tikitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing

cri

A ran 24 ga wata, cibiyar sayar da tikitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta bayar da labari cewa, tun da aka fara sayar da tikitin gasar a mataki na biyu, an riga an samu takardun odar tikitin dubu 340, inda ake son sayen tikitoci fiye da miliyan 2 da dubu 20 na gasar.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, an gabatar da wadannan takardun odar tikiti da yawansu ya kai kashi 90 cikin kashi a kan shafin internet na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. A waje daya, takardun odar tikiti da mazaunan birnin Beijing suka gabatar sun fi sauran wuraren kasar Sin yawa, wato yawan takardun odar tikiti da mazaunan birnin Beijing suka gabatar ya kai fiye da dubu 180.

Jagoran cibiyar sayar da tikitin gasar ya bayyana cewa, yawan tikitocin da suke shafar gasar wasannin kundunbala da lankwashe-lankwashe da wasan Pinpon da gasar tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali da gasar ninkaya da ake son saye ya riga ya wuce yawan tikitocinsu da za a iya sayarwa. Bugu da kari kuma, an fi son sayen tikitoci na gasar kwallon kwando ta maza da gasar maza ta karshe ta gudun tsallake-tsallake na mita 110 da gasar kwallon Pinpon ta karshe ta tsakanin namiji da namiji. (Sanusi Chen)