Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-24 15:46:28    
Ana raya yankin bunkasa tattalin arziki da fasaha ta birnin Xining a arewa maso yammacin kasar Sin

cri

Birnin Xining shi ne fadar gwamnatin lardin Qinghai da ke a arewa maso yammacin kasar Sin. An kaddamar da yankin bunkasa tattalin arziki da fasaha ta birnin Xining ne a watan Yuli na shekarar 2000. Bisa kokarin da aka yi ta yi a cikin shekaru 7 da suka wuce, yanzu an riga an kafa wani kyakkyawan tsarin masana'antu a yankin wanda masana'antun narke karafa da na sarrafa magunguna da gyaran na'urori da amfanin gona da yin kayayyakin gine-gine da hada magunguna irin na abubuwa masu rai ke zama ginshikinsa. Yawan masana'antu a yankin ya wuce 500, jimlar kudin da aka zuba kuma ya wuce kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 10, haka kuma yawan mutanen da aka dauke su aiki ma ya kai misalin dubu 20.

Malam Chen Zhizhong, mataimakin shugaban hukumar kula da tsare-tsaren tattalin arziki ta lardin Qinghai ya bayyana cewa, ta hanyar raya yankin nan na brinin Xining, an gaggauta bunkasa aikin masana'antu a duk lardin Qinghai. Ya ce, "a shekarun nan, an bunkasa aikin masana'antu da kyau a duk lardin Qinghai. Yawan kudin da aka samu daga wajen manyan masana'antu ya karu da kudin Sin Yuan biliyan 24 da miliyan 30 a duk lardin, an iya samu irin wannan ci gaba ne duk bisa taimakon da aka samu daga bunkasuwar masana'antu a manyan wurare, musamman ma saurin bukasuwar masana'antu ya kai kashi 25.5 cikin dari a birnin Xining, ya kai matsayin farko a dukkan lardin."

Yanzu, yankin ya riga ya zama hanyar da ake bi wajen yin hadin kai a tsakanin lardin Qinghai da Taiwan na kasar Sin. Babban kamfanin yin aikin injiniyar abubuwa masu rai da ake kira Mingxing a lardin Qinghai wani kamfani ne da 'yan kasuwa na Taiwan suka zuba masa jari. Malam Zhao Xia, babban manajan wannan kamfani wanda ya fito daga Taiwan, ya bayyana cewa, "na yi shekaru hudu ina zama a birnin Xining. Ko da yake lardin Qinghai ba shi da arziki sosai ba, amma yana da babban burinsa na neman samun bunkasuwa. Da zuciya daya, gwamnatin lardin take kyakkyawar maraba da 'yan kasuwa su zuba jari a lardin. Gwamnatin tana dora muhimmanci sosai ga yankin bunkasa tattalin arziki da fasaha na birnin Xining, tana aiwatar da manufar nuna gatanci a wasu fannoni, a bangare daya kuma manufar da ake aiwatarwa game da ba da hidima a yankin ta fi sauran unguwoyin birnin da yankunansa kyau, sabo da haka hukumomin kula da harkokin yankin suna samar da hidima ne a dukkan fannoni."

A shekarun nan da suka gabata, lardin Qinghai ya kara kyautata manufofinsa game da raya yankin bunkasa tattalin arziki da fasaha, ya gaggauta shigo da kyawawan ayyuka daga kasashen waje. Malam Chen Zhizhong, mataimakin shugaban hukumar kula da tsare-tsaren tattalin arziki ta lardin Qinghai ya ce, "gwamnatin lardin ta inganta yankin bunkasa tattalin arziki da fasaha ta birnin Xining, ta bi sabbin hanyoyin kula da yanki ta hanyoyi daban daban, don haka an bunkasa tattalin arzikin yanki cikin sauri kuma a fannoni daban daban. Sakamakon da muka samu shi ne, gwamnatin ta nuna himma ga tsaida manufofi, kullum hukumomin suna samar da kyakkyawar hidima, masana'antu sun dau niyyar samun bunkasuwa, kuma jama'ar suna cike da imani."

Bisa kimantawar da aka yi, an ce, zuwa shekarar 2010, jimlar kudin da za a samu daga wajen samar da kayayyaki a yankin zai karu zuwa kudin Sin Yuan biliyan 13.5, yawan mutanen da za a dauke su aiki kuma zai wuce dubu 50. A sakamakon ci gaba da ake samu wajen bunkasa yankin, ba da dadewa ba za a bunkasa tattalin arzikin masana'antu a lardin Qinghai cikin sauri kwarai. (Halilu)