Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-24 15:45:09    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- A ran 29 ga watan Nuwamba, an bude taron "dadalin fadin albarkacin bakinka kan batun bunkasa jihar Tibet ta kasar Sin" a karo na farko a birnin Vienna, hedkwatar kasar Austria. Wannan ya zama karo na farko ke nan da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin da kungiyar Austria kan ci gaban dangantakar tattalin arziki a tsakanin Austrir da kasar Sin suka shirya wannan taron dandalin kara wa juna sani ta hanyar hadin gwiwa, babban take na wannan taro kuma shi ne bunkasa jihar Tibet ta kasar Sin.

Wakilai fiye da 200 da suka zo daga sassan siyasa da tattalin arziki da al'adu da ba da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasashen 2 wato Sin da Austria sun halarci bikin bude dandalin. Cikin sakon taya murna da Mr. Michael Spindelegger, mataimakin shugaba na farko na majalisar dokoki ta Austria ya aike da shi ya bayyana cewa, "dadalin fadi albarkacin bakinka kan batun bunkasa jihar Tibet ta kasar Sin" zai sa 'yan kabilar Tibet da ke kasar Austria su yi alfahari, kuma zai ba da taimako ga kara fahintar juna da yin mu'amala tsakanin jama'ar kasashen 2 wajen tunani.

---- Yau da shekaru 50 ke nan da aka kaddamar da babbakun kabilar Zhuang, wato wani irin yare daya kawai wanda ya samu amincewa daga wajen gwamnatin kasar Sin. Kwanan baya a birnin Nanning, hedkwatar jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudancin kasar, an yi taron tunawa da ranar cika shekaru 50 da kaddamar da "tsarin babbakun kabilar Zhuang".

Kabilar Zhuang, wata karamar kabila ce wadda ta ke da mutane mafi yawa a tsakanin kananan kabilun kasar Sin. 'yan kabilar suna yin amfani da harshen kabilar kaka da kakanni, amma tsohun harshen kabilar ba shi da kyau sosai, ba za a iya yada shi da yin amfani da shi ko ina ba. Sabo da haka a watan Nuwamba na shekarar 1957, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tattauna kuma ta zartas da "Tsarin babbakun kabilar Zhuang" wanda ya samu tabbatuwa daga wajen kwararrun kasar Sin da na kasashen waje, kuma an yarda da yin amfani da shi a shiyyoin da 'yan kabilar Zhuang ke zama.

A gun taron, Mr. Chen Wu, mataimakin shugaban gwamnatin jihar Guangxi ta kabilar Zhang mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, "Tsarin babbakun kabilar Zhuang" da aka tanada ya sa aya ga tarihin rashin samun babbaku iri daya ga duk 'yan kabilar ta hanyar kimiyya wadanda kuma suka dace da harshen kabilar, aikin nan ya kago shuruda masu amfani ga 'yan kabilar don yin mu'amala a tsakaninsu da mutanen kasashen duniya.

'Yan kabilar Zhuang musamman suna zama a jihar Guangxi da lardin Yunnan da sauran wasu wurare, yawan su da ke jihar Guangxi kuma ya wuce miliyan 17.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)