Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-21 19:03:45    
Hukumar Sichuan ta dauki mtakai domin tabatar da ingancin amfanin gona

cri

Yanzu batun ingancin amfanin gona ya jawo hankulan rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar Sin sosai. Yaya za a tabbatar da ingancin amfanin gona? Gudanar da dukkan matakai na aikin gona bisa ma'aunin da aka tsara wata hanya ce da ta zama wajaba. Lardin Sichuan, wanda ke daya daga cikin muhimman lardunan kasar Sin a fannin aikin gona, ya zama kan gaba a kasar Sin a fannin aiwatar da tsarin kula da daidaiton ingancin aikin gona.

An sami wani sansanin noman albasa irin na kasar Sin mai fadin kadada misalin 10 a gundumar Shizhong na birnin Leshan na lardin Sichuan. Shi ne sansani na wani kamfanin sarrafawa da fitar da abinci ta Leshan. Sansanin da kamfanin sun daddale yarjejeniyar samar da danyun amfanin gona, sansanin ya noma amfanin gona bisa ma'aunin da kamfanin ya tsara, ya kuma samar wa kamfanin danyun amfanin gona a ko wace rana, wadanda suka dace da bukatun kamfanin a fannonin yawa da inganci. Kamfanin kuwa ya sarrafa danyun amfanin gona ya sayar da su zuwa ketare.

Zhou Zhiwu, wani manoni kuma mai kula da wannan sansani ya bayyana cewa, a tsanake ne sansanin yake samar da amfanin gona bisa ma'aunin da kamfanin ya tsara. Ya ce,'Muna gudanar da dukkan ayyuka bisa ma'aunin kamfanin, har ma zuba taki. Mun zuba takin da kamfanin yake bukata. Ba mu sayi takin da muke so ba. Bayan da muka mika rahoto ga kamfanin kan mtsalolin kwari da cututtukan amfanin gona, kamfanin ya kan tura masu fasaha zuwa sansaninmu. Su kan ba da magani bayan da suka dudduba.'

Zhang Qiang, shugaban hukumar kula da aikin gona ta gundumar Shizhong ya yi bayani kan dalilin da ya sa a bi wannan hanya wajen tafiyar da sansanin a yanzu, ya ce, 'Dalilin shi ne maganin kashe kwari da aka hana amfani da shi a kasar Japan. A kasarmu an yi na'am da duddubawar da aka yi wa irin wannan magani, amma bisa ma'aunin da Japan ta tsara a fannin duddubawa, ya wuce ma'aunin. A karshe dai, kamfanin ya yi asarar kudin Sin misalin yuan miliyan 3 kai tsaye. Sa'an nan kuma, bangaren Japan ya bukaci ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da a ba shi diyya. Ta haka kamfanin ya yi asarar kudin Sin misalin yuan miliyan 10. A gaskiya, a dukkan wuraren da suka samar da danyun amfanin gona, wani manomi kawai ya yi amfani da irin wannan magani a kan gona mai fadin kadada misalin 0.2.'

Saboda haka in an nemi rage hasara, wajibi ne a daga matsayin daidaiton ingancin aikin gona, a kula da gonaki yadda ya kamata. Ta haka, hukumar gundumar Shizhong ta gabatar da wata hanya, wato an kafa sansani a tsakanin kamfani da manoma, masu kula da sansani sun noma amfanin gona bisa ma'aunin bai daya.

Wu Xicheng, shugaban wani kamfani da ke sarrafawa da kuma sayar da amfanin gona zuwa ketare ya yi hasashen cewa, rarraba gonaki domin yin noma bai dace da ci gaban zaman al'ummar kasa ba. Tattara gonaki tare ya ba da taimako wajen daidaiton ingancin amfanin gona. Ya ce, 'Mun fito da tsarin kula da ayyuka. Bisa wannan tsari, mun iya binciken irin da manoma suka sayi, da huda gonaki da kashe kwayoyi da dasa iri da ba da taki da yin ban ruwa da kuma mutanen da suka kula da gonakin. In an kasance da matsalar ingancin amfanin gona, nan da nan za mu tono gonakin da aka samu irin wannan amfanin gona.'

Ayyukan da ake yi a birnin Leshan wani bangare ne na ayyukan da hukumar lardin Sichuan take yi wajen aiwatar da tsarin kula da daidaiton ingancin amfanin gona. Tun daga shekarar 2005, hukumar lardin Sichuan ya fara raya sansanoni bisa ma'auni, yanzu ta kafa sansanoni fiye da 80 fiye da ma'auni da hukumomi na matsayi daban daban suka amince da su, wanda fadinsu ya kai kashi 30 cikin kashi dari bisa na gonakin lardin. Nan gaba lardin Sichuan zai kyautata tsarin sa ido da bincike a fannin ayyukan daidaiton ingancin amfanin gona, zai kuma kara horar da manoma ta fuskar ilmi da ba su hidimomi, ta haka za a kara tabbatar da ingancin amfanin gona.(Tasallah)