Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-21 18:04:21    
Gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya da CRI ta gudanar a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing (Babi na hudu)

cri

Bayani kan biranen da suka bada taimako wajen gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka sani cewa, za a gudanar da taron wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 tsakanin ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Domin samar muku da wata kyakkyawar damar kara samun ilmi da kuma sa hannu cikin harkokin taron wasannin, tun daga yau wato ran 9 ga watan da muke ciki, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya kaddamar da gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya a game da ilmin taron wasannin Olympics na Beijing, wadda ke da lakabi haka: " Mu hadu a shekarar 2008" ta hanyar yin amfani da harsunan waje 38, da Sinanci, kare-karen harsuna iri 4 na wuraren kasar Sin da kuma tashar internet wato www. cri.com.cn.

Gasar nan za ta dauki rabin shekara. A cikin wannan lokaci dai, za mu watsa bayanan musamman guda 4 na game da taron wasannin Olympic daya bayan daya; kuma a karshen kowane bayanin musamman, akwai tambayoyi guda biyu game da taron wasannin. To, za ku iya shiga wannan gasa ta hanyar sauraron shirye-shiryenmu. Abin da ya fi burge aminai masu sauraronmu shi ne, duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman, za su iya kawo ziyara nan Beijing a watan Yuni na shekara mai zuwa.

Jama'a masu sauraronmu, a makon jiya dai, mun karanta muku bayanin musamman na uku a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing, wanda ke da lakabi haka: " Bayani kan filaye da dakunan wasa na gasar wasannin Olympics ta Beijing. Yau, za mu kawo muku bayanin musamman na hudu wato na karshe dangane da wannan gagarumar gasa. Kanun bayanin shi ne: " Bayani kan biranen da suka bada taimako wajen gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing".

Aminai masu sauraro, bisa bukatun shirye-shiryen gasannin da aka tsara, ba birnin Beijing ne daya tilo, inda za a gudanar da gasar wasannin Olympics a shekarar 2008 ba, wato ke nan za a gudanar da wasu gasanni a birnin Tianjin, Qinhuangdao, Shanghai da kuma birnin Shenyang na kasar Sin. Ban da wannan kuma, birnin Qingdao ya dauki bakuncin gasar tseren kwale-kwale da kuma wasu dangoginta; Kazalika, za a gudanar da dukkan gasannin sukuwar dawaki a yankin Hongkong na kasar Sin. Ko da yake wadannan birane ba muhimman wurare, inda za a gudanar da gasar wasannin Olympics ba, amma babu tantama, za a rubuta sunayensu cikin tarihin wasannin Olympics na duniya.

Aminai, sanin kowa ne, wasan kwale-kwale, wani irin wasa ne na gasar wasannin Olympics, wanda akan gudanar da shi cikin teku. Saboda haka, duk wata kasa maras mafita ta teku dake daukar nauyin gudanar da irin wanna gasa, dole ne ta zabi wani birnin dake bakin teku don gudanar da shi. Gwamnatin birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin ta yi alfaharin samun damar gudanar da irin wannan gasa mai ban sha'awa a shekara mai zuwa. Magajin birnin mai suna Xia Geng ya furta cewa: " Mun samu saurin bunkasuwar tattalin arziki a 'yan shekarun baya bisa karfin ingizawar yunkurin share fagen gasar wasannin Olympics, wadda kuma ta kawo wa mazauna birnin moriya a fannoni da dama".

Bisa alkaluman da aka bayar an ce, cikin shekaru huda da suka gabata, gwamnatin birnin ta zuba makudan kudade da yawansu ya kai kudin Sin wato RMB Yuan kimanin biliyan 20 wajen tafiyar da muhimman ayyukan gine-gine kamar na haka dogon rami a karkashin teku, da gina babbar gada kan teku da kuma yin kwaskwarimar filin saukar jirgin sama da dai sauransu.

Aminai masu sauraronmu, wasan sukuwar dawaki, wani irin wasa ne taya tak wanda wani dan wasa da kuma wata dabba sukan nuna tare dake cikin dukkan ayyukan wasanni guda 28 na gasar wasannin Olympics. Saboda haka, irin wannan wasa na da sha'awa sosai, wanda yakan yi wa 'yan kallo gamon katar. Mazauna yankin Hongkong suna sha'awar wasan sukuwar dawaki kwarai da gaske. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na Hongkong, Mr. Timothy Fok ya fadi cewa: " Gudanar da gasar sukuwar dawaki a yankin Hongkong zai sa kaimi ga mazauna yankin wajen kara kaunar kasar mahaifa. Idan aka gudanar da irin wannan gasa cikin nasara a wannan yanki, to labudda zai kara bunkasa sha'anin wasan motsa jiki na Hogkong da kuma taka rawar gani ga samari matasa na yankin wajen yin matukar kokari tare da mazauna birnin Beijing wato hedkwatar kasar mahaifa don gudanar da gagarumar gasar wasannin Olympics kafada da kafada".

An kammala gina filayen gasar sukuwar dawaki da kuma dakunan horo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing a ran 7 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, wadanda suka samu yabo sosai daga 'yan wasa na yankuna daban-daban na duniya yayin da suke halartar gasar jarrabawar sukuwar dawaki da aka gudanar a watan Agusta na wannan shekara.

Aminai masu sauraro, gasar wasan kwallon kafa, wata gasa ce da ta fi daukar dogon lokaci cikin ajandar gasannin Olympics. Domin saukaka shirye-shiryen ajandar gasannin, akan kafa rassan filayen wasan kwallon kafa a waje da babban filin wasa. To, birnin Shanghai ya yi alfaharin samun damar gudanar da wasu gasannin kwallon kafa a shekara mai kamawa. Magajin birnin Shanghai Mr. Han Zheng yana mai cewa: " A ganina, wani birni na zamani kamar Shanghai dake bude kofa ga kasashen waje, kamata ya yi ya gwada sabuwar fuska kyakkyawa ta kasarmu ta hanyar gudanar da irin wadannan gasanni".

Aminai masu sauraro, kafin mu kawo karshen bayanin musamman na yau, bari in shaida muku tambayoyi guda biyu. Tambaya ta farko ita ce: Wadanne birane guda shida na kasar Sin da za su bada taimako ga gudanar gasar wasannin Olympics ta Beijing? Tambaya ta biyu ita ce: wace irin gasa ce yankin Hongkong zai dauki bakuncinta a lokacin gasar gasannin Olympics ta Beijing?

To, madalla jama'a masu sauraronmu,duka-duka bayanan musamman ke nan da muka kawo muku a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. Muna muku kyakkyawan fatan samun maki mai gamsarwa cikin gasar kuma ku ba mu amsa cikin lokaci. ( Sani Wang )