Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 16:53:12    
Kamfanin Hua Wei na kasar Sin ya zama kamfanin samar da kayayyaki cikin hadin gwiwa da ya fi girma a fannin ba da hidimar giza-gizan sadarwa a lokacin aikin haji

cri

A shekarar da muke ciki, kamfanin Hua Wei na kasar Sin ya zama kamfanin samar da kayayyaki cikin hadin gwiwa da ya fi girma a fannin ba da hidimar giza-gizan sadarwa a lokacin aikin haji.

To, masu sauraro, yanzu bari mu ci gaba da shirinmu na yau na zaman rayuwar musulmi na kasar Sin.

Bisa labarin da muka samu daga wani jami'i na reshen kamfanin fasaha na Hua Wei na kasar Sin da ke kasar Saudi Arabia, an ce, kamfanin ya riga ya zama kamfanin samar da kayayyaki cikin hadin gwiwa da ya fi girma na kasar Saudu Arabia a fannin ba da hidimar giza-gizan sadarwa a lokacin aikin haji.

Bisa kusantowar lokacin yin haji na musulmi a wannan shekara, hukumomin sadarwa na garin Mekka da ke yammacin kasar Saudi Arabia, suna kara yalwata na'u'rori da kuma yin gyare-gyare cikin gaggawa. An ce, a matsayinsa na muhimmiyar abokiyar hada kai ta hukumomin sadarwa na Saudi Arabia, a shekarar da muke ciki, kamfanin Hua Wei ya samu rinjaye bisa na sauran 'yan takara na duniya a fannonin samar da na'uro'i, da sansani, da kuma ba da hidimar giza-gizan sadarwa, a sakamakon haka, ya samu yawancin rabe-raben kasuwar kasar wajen ba da hidimar sadarwa a lokacin aikin haji.

Masu aikin fasaha na kamfanin Hua Wei sun gabatar da cewa, a lokacin yin haji, mutane kusan miliyan 3 da ke Mekka, wanda fadinsa ya kai fiye da muraba'in kilomita goma, za su buga waya na gida da ketare, har ma wasu za su buga waya ta taliho ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, saboda haka, wannan ne jarrabawar da kamfanin Hua Wei zai fuskanta. Kamfanin Hua Wei ya riga ya aika da kwararru da su tsara da kuma dudduba giza-gizan sadarwa a obataya, don tabbatar da aikin na'u'ro'i kamar yadda ya kamata. Hukumomin da abin ya shafa na Saudi Arabia sun bayyana cewa, za su gabatar da wannan abin al'ajabi don neman shiga bajintar duniya ta Guinness, bayan da aka kawo karshen yanayin yin haji na bana.

Shugaban garin fasahar Sarki Abdulah Aziz na Saudi Arabia, wato wani abokin hadin gwiwa na kamfanin Hua Wei da ke wurin, Mr. Muhammed Suweili ya bayyana cewa, kamfanin Hua Wei na kasar Sin ya samu saurin bunkasuwa a kasuwar Saudi Arabia, yana da boyayen karfi. Bayan haka kuma, ya nuna yabo sosai ga kamfanin Hua Wei, saboda yana mai da hankali kan amfana wa rayuwar jama'a, kuma yana sa kaimi ga hada kai tare da hukumomin kimiyya da fasaha, da ba da ilmi na Saudi Arabia wajen horar da kwararru, Mr. Suweili ya ce, yana fatan kara habaka da kuma zurfafa hadin gwiwa ta irin nan.

Bisa labarin da muka samu an ce, kamfanin Hua Wei ya soma shiga kasuwar Saudi Arabia tun daga shekarar 1999, yanzu yana hadin gwiwa tare da kamfanin STC, da na MOBILY, wato kamfanoni guda biyu da suka fi girma a kasar Saudi Arabia a fannin sadarwa.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau ke nan, muna fata kun ji dadinsa, a nan Bilkisu ke cewa, sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.