Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 16:50:53    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin(14)

cri

Nauyin aiki da na gida ya gagari wani mutum, An sami wani mutum mai shekaru kimanin talatin a gundumar Hulin ta lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin.Wata rana da ya shiga wani gidan waya ya ga wata yarinya mai shekaru kimanin shida,hankalinsa ya fita yana so ya tilasta yarinya ta tafi tare da shi.sauran matafiya kusa da shi,suka ce zai kashe yarinyar ne. Daga baya aka kirawo 'yan sanda suka zo,da isowarsu sai suka lallashe shi da ya ajiye wukar.Daga bisani ya yi saranda. Wannan mutum da ya sace yarinyar ya ce ya yi hakan nan ne domin nauyin aiki da na harkokin gida ya gagare shi wato yana so ya jawo hankulan mutane da yin haka.Daga baya an kai shi caji ofisi domin cigaba da binciken batun.

Uba bai ji dadin matsayinsa a gida ba. Wata ma'aikaciya a ofishin wata ma'aikata a birnin Shanghai tana son kare kwarai da gaske,har ma ta aika da kudin Sin Yuan dari hudu kowane wata zuwa ga mahaifinta a birnin Dalian na lardin Liaoning domin kula da karen da take so. Mahaifinta ya ce "hankalina ya gaza kwantawa saboda diyata ta ba ni aikin kula da kare.Ko wace rana sau biyu sai na fita waje da kare." Ya kuma ci gaba da cewa" ban da wannan kuma ta ba ni kudin Sin Yuan dari biyar domin in sayi abinci domin karen da take so. Duk lokacin da ta buga mini waya,abu na farko da take fara tambaya shi ne lafiyar karen,na biyu kuwa nawa."

----Kyautar kudi ga wanda ya iya zana siffar kifi. An sami wani mutum mai suna Wang a wani kauye na gundumar Huichun na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin. Ranar talata da ta shige,malam Wang ya gano kudin Sin Yuan dubu uku a cikin wani kifin da ya lalace wanda ya karensa ya dauko daga juji.Yayin da ya ga karensa na cin kifi ya yi mamaki, sai ya je wurin ya gano ashe kudin Sin Yuan dubu uku ne a dunkulle a halin yanzu.yana so ya mayar da kudin ga mai kifin. Ya yi tsammani watakila kifin nan kyauta ce da aka ba wani.kuma da ya ga kifin ya lalace sai ya jefa shi cikin juji.Don haka ya ce duk mutumin da ya zana siffar kifin sosai,to zai mayar da kudin gare shi.

Sunan masoyiyarsa ya yi daidai da sunan mamasa. An samu wata budurwa a gundumar Kengli ta lardin Shandong dake gabashin kasar Sin da ya kamata ta canja sunanta domin samun amincewar surukarta.Sunan budurwa shi ne Li Fang tana da shekaru 21 da haihuwa.Ta samu masoyinta Mr Wang ne a wurin aiki a watan Mayu da ya gabata.Sun yi shirin aure a shekara mai zuwa.Da farko sai suka samu amincewa daga iyayensu. Mamar Wang ta ce ba za ta yarda da wannan aure ba sai budurwa ta canza sunanta saboda sunanta ya yi daidai da nawa.

A zamanin da an haramta aure tsakanin 'ya'yan iyalai masu suna bai daya. A ganinsu rashin sa'a da da'a ne. Bayan budurwa ta yi dogon tunani ta ce za ta canza sunanta.

Kyautar ta zama masifa. Wani saurayi ne ya boye zoben zinariya a cikin cake na murnar ranar haihuwar kakarsa,da kakarsa ba ta san abun da ke ciki ba ta yi farin ciki ta hadiye shi gaba daya. Da ta ji zafi sai nan da nan aka kai ta asibiti domin yin fida. Wannan al'amari ya faru ne a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.Sunan kakar Li,an shirya mata liyafa ne a gidan cin abinci a ranar lahadi domin murnar ranar haihuwarta ta 76.Jikanta ya kawo mata cake din ranar haihuwa kafin ya ce wani abu sai kakarsa ta cinye cake dake hade da zoben zinariya.Nan da nan jikanta ta kai ta asibiti domin a yi mata fida.Daga bisani kakar ta samu koshin lafiya.

Zama yadda ya kamata ya kara tsawon rai.Wani tsoho mai shekaru sama da dari da haihuwa da surukinsa sun samu asirin samun tsawon rai a birnin Nanjing na lardin Jiangsu na kasar Sin. Sunan tsohon nan Guo Cairu wanda ya ke da shekaru 107 da haihuwa,ya zama mutum da kowa ya sani bayan da ya taka wata rawa a cikin sinimar da aka dauka domin neman damar shirya wasannin Olympic na Beijing a shekara ta 2001. Ko da ya ke ya tsufa,yana da saurin tunani da kishin zirga zirga da wani wasan motsa jiki na gargajiya,ko wace rana ya kan yi wannan wasa. A karkashin inuwarsa surukinsa Du Yeren shi ma ya koyi fasahar rubutu bayan ya yi ritaya.Ga shi yanzu ana iya ganin rubutunsa a wuraren shakatawa da yawa na birnin. Asirin samun tsawon rai dai shi ne kasancewa da kuruciya a zuci da fara wani aikin da kake da sha'awa a kai.