Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-19 21:00:23    
Samun kiba fiye da kima ya yi illa sosai ga lafiyar jikin dan Adam

cri

Bayan da masu aikin likitanci na kasar Amurka suka gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci, sun gano cewa, yaran da ke samun kiba fiye da kima sun fi saukin kamuwa da cututtukan kafa idan an kwatanta su da yaran da ke da nauyin jiki kamar yadda ya kamata.

Kwararren kasar Amurka a fannin aikin likitanci Daryl Hickok da abokan aikinsa sun bayar da wani rahoto, inda suka nuna cewa, idan yara sun samu kiba fiye da kima, to kafafunsu da suke girma za su dauki nauyi da kuma matsi fiye da kima, wanda zai iya lalata kafafunsu sosai.

Haka kuma Mr. Hickok ya bayyana cewa, kullum kafafun yara mata su kan girma kamar yadda ya kamata lokacin da shekarunsu ya kai 14 zuwa 15 da haihuwa, amma kullum kafafun yara maza su kan girma kamar yadda ya kamata lokacin da shekarunsu ya kai 15 zuwa 17 da haihuwa. Kafin wannan, kasusuwan kafafun yara sun fi saukin lalata sakamakon samun kiba fiye da kima, ta haka wadannan yara sun fi saukin kamuwa da cutar doron kafa da dai sauran cututtukan kafa.

Ban da wannan kuma wannan kwararre ya nuna cewa, a da yaran da ke son wasannin motsa jiki sosai su kan kamu da wadannan cututtukan da muka ambata a baya, amma yanzu yaran da ke samun kiba fiye da kima masu yawa suna kamuwa da cututtukan. Bayan da yaran da ke da kiba fiye da kima sun kamu da cututtukan kafa, su kan rage lokutan motsa jiki sakamakon jin zafin kafafunsu, wanda zai iya haddasa ci gaban karuwar nauyin jikinsu, ta haka wannan zai zama wani mumunan abu da ke faruwa.

Mr. Hickok yana ganin cewa, yaran da ke kamuwa da cututtukan kafa suna iya sa takalman musamman wajen gyara kafafunsu, kuma idan halin da suke ciki ya tsananata, to ana iya yin wa kafafunsu tiyata.

Ban da wannan kuma, bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Faransa suka yi bincike, sun gano cewa, ba kawai samun kiba fiye da kima zai kara hadarin kamuwa da cututtukan kafa ba, har ma zai iya rage basirar mutane.

Bisa labarin da wata jaridar kasar Birtaniya ta bayar, an ce, masu ilmin kimiyya na kasar Faransa sun gudanar da wata jarrabawar basira har ta tsawon shekaru biyar ga baligai fiye da 2200 da shekarunsu ya kai 32 zuwa 62 da haihuwa. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, a cikin kalmomin da ake cikin jarrabawar, mutanen da ke da jiki sosai suna iya tuna da kalmomin da yawansu ya kai 56 bisa dari, amma mutanen da ke samun kiba fiye da kima suna iya tuna da kalmomin da yawansu ya kai 44 bisa dari kawai.

Bayan da manazarta na kasar Amurka suka gudanar da wani sabon bincike, sun gano cewa, mutanen da suke da kiba fiye da kima sun fi saukin jin raunuka a cikin ayyukansu idan an kwatanta su da wadanda suke da jiki sosai.

Bisa bayanan da kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka bayar, an ce, manazarta na kwalejin kiwon lafiyar jama'a na Bloomberg na jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga ma'aikata na masana'antu 8 da ke samar da kayayyakin sinadarin aluminium wajen halin ayyuka da suke ciki, daga baya kuma sun samu sakamakon da muka ambata a baya.

Manazarta sun kasa wadannan ma'aikata cikin kungiyoyi biyar, wato kungiyar da ke da siraran mutane, da kungiyar da ke da mutanen da suke da jiki sosai, da kungiyar da ke da mutanen da suke da kiba kadan, da wadda take da mutanen da suke da dan kiba sosai, da kuma wadda take da mutanen da suke da kiba fiye da kima. A cikin ma'aikata 7690 da aka gudanar da binciken a kansu, kashi 29 cikin dari sun taba jin raunuka a kalla sau daya sakamakon ayyukansu daga shekara ta 2000 zuwa shekara ta 2004. Haka kuma a cikin wadannan mutanen da suka ji raunuka, kashi 30 cikin dari suna da kiba kadan ko kuma suna da dan kiba sosai, kuma kashi 34 cikin dari daga cikinsu suna da kiba fiye da kima.

Ban da wannan kuma binciken ya gano cewa, game da mutanen da suke da kiba kadan ko kuma sosai, bangaren jikinsu da ya fi saukin jin rauni shi ne hannayensu. Amma game da mutanen da suke da kiba fiye da kima, bangaren jikinsu da suka fi saukin jin rauni su ne kafofinsu da kuma gwiwoyinsu. (Kande Gao)