A dakalin nuna wasannin kwaikwayo cikin wake-wake da kide-kide na duniya, Zhang Liping ta kasar Sin ita ce shahararriyar zabiya a matsayin farko. Ta jawo hankulan 'yan kallo na wurare daban daban na duniya ta hanyar wakokin da ta rera da tattausar murya da nagartattun fasahohin nuna wasanni .
A watan Maris na shekarar 2004, Zabiya Zhang Liping ta zama babbar 'yar wasan kwaikwayo da aka yi tare da wake-wake da kide-kide kuma mai suna "Madam butterfly" a babban gida mafi girma na nuna wasannin kwaikwayo wato a gidan wasa na "The Metropolitan Opera House dake New York", inda ta sami yabo sosai da sosai. Game da gidan wasan nan na kasar Amurka, sai nagartattun 'yan wasan kwaikwayo da ke bisa matsayin farko ne za su iya samun damar nuna wasanni a wurin, amma fasahar nuna wasannin da Zhang Liping ta yi ta sanya 'yan kallon kasashen waje suka fahimci fasahar wasanni da 'yar wasan kasar Sin ta yi. Saboda chaka a lokacin da ta fito don nuna godiya ga 'yan kallo a dakalin nuna wasanni, sai 'yan kallo suka yi mata tafi raf raf har cikin mintoci 20. wannan ba a taba gani ba a gidan.
An haifi zabiya Zhang Liping a lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin, tana da shekaru 40 da haihuwa, a lokacin da take karama, tana kaunar rera wakoki da raye-raye sosai, amma ba ta taba yin wasannin kwaikwayo tare da wake-wake da kide-kide ba, bisa tasirin mahaifinta ne, take kaunar wasan Opera, Zhang Liping ta bayyana cewa, a lokacin da nake karama, na sani cewa, mahaifina yana kaunar wasan Opera, saboda haka ya kan tafi kallon wasan Opera tare da ni, a gaskiya dai na taba kallon irin wasan ba sau daya ba sau biyu ba, amma idan na sami dama, to dole ne na je kallon wasan, kuma ina son rera wake-waken wasan Opera.
Karo na farko da Zhang Liping ta je kallon wasan kwaikwayo da aka nuna ta hanyar wake-wake da kide-kide ne a lokacin da ta kai shekaru fiye da goma da haihuwa, tana kallon wasan kwaikwayo da ake kira "The Lady of the Camellias", wasan ya burge ta burge sosai da sosai kodayake ba ta fahimci abubuwan da aka bayyana a cikin wasan ba, amma da ta je ta kalla, sai da ta yi kuka sosai, har ta ji cewa, wasan na da kyau sosai. Daga nan sai ta soma kaunar wasan kwaikwayon da aka nuna ta hanyar wake-wake da kide-kide.
A shekarar 1989, Zhang Liping ta kammala karatu a jami'ar koyar da ilmin wake-wake da kide-kide ta tsakiya ta kasar Sin, A shekarar 1990, ta yi dalibta a kasar Canada, bayan da ta kammala karatu a jami'ar Canada, sai ta nuna wasanni a gidan nuna wasannin fasaha na birnin Vancouver, inda ta sami nasara sosai. A shekarar 2004, karo na farko ne aka gayyace ta don nuna wasan kwaikwayo mai suna "Madam buttrerfly" a gidan wasa na "The Metropolitan Opera Hause da ke New York". Zabiya Zhang Liping ta bayyana cewa, ba fasahar nuna wasanni ta burge mutane ba, amma wakokin da aka rera ne suka burge mutane sosai da sosai, domin rera wakoki da zuciya na da bambanci da rera wakoki da fasaha, 'yan kallo suna iya bambanta su sosai.
Zhang Liping ta burge 'yan kallo na kasashe daban daban na duniya ta hanyar tausayar muryarta mai dadin ji sosai, kuma ta taba nuna wasannin kwaikayo tare da wake-wake da kide-kide har fiye da 20, a ko'ina da ta sa kafa, sai ta sami yabo sosai da sosai.
Zhang Liping tana kan nuna wasanni a kasashe daban daban na duniya, ta taba zama babbar 'yar wasa a cikin wasanni da yawa, kuma ta gamu da wahaloli da yawa, abin da ta mai da hankali a kai shi ne yadda za ta nuna wasanni yadda ya kamata domin 'yan kallo.
Zhang Liping tana nuna wasanni a kasashen waje cikin watanni 7 zuwa watanni 8 a shekara daya, har ta kai ba ta da lokacin kula da yaronta , amma danta ya gaya mata cewa, ba kome, babbansa da kakarsa suna iya kula da shi sosai da sosai. Da ta ji maganar, sai abin ya gurge ta sosai har da hawaye.
A shekarar 2006, Zhang Liping ta koma gida ta sami aikin koyarwa a jami'ar koyar da ilmin wake-wake da kide-kide ta tsakiya ta kasar Sin, kuma tana kokarin horar da dalibai don su iya zama nagartattun 'yan wasa, a sa'I daya kuma ta koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasashen yamma don sanya mutanen kasar Sin su kara fahimtar wasannin kwaikwayo na kasashen yamma.(Halima)
|