Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-19 08:15:49    
Kungiyar `yan wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta karbi sakamakon zaben da aka yi ta hanyar yin canki-canki yadda ya kamata

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,aka sanar da sakamakon zaben da aka yi ta hanyar yin canki-canki domin shiga gasar zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta kasar Afirka ta kudu ta shekarar 2010.A gun gasar zagaye na farko da za a shirya a shiyyar Asiya,kungiyar kasar Sin tana cikin rukuni na farko tare da wasu kungiyoyi masu karfi wadanda ke hada da kungiyar kasar Australia da ta kasar Iraki da kuma ta kasar Qatar.Game da wannan,ra`ayin bainal jama`a yana ganin cewa,kungiyar kasar Sin ta gamu da wahala,amma `yan wasa da malaman koyar da wasa na kungiyar kasar Sin ba su yarda da wannan ra`ayi ba,a banban da haka,sun nuna kwazo da himma suna yin kokari domin yin aikin share fage.

A ran 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2007,a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu,aka shirya bikin yin canki-canki na gasar zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta kasar Afirka ta kudu ta shekarar 2010.Bisa tsarin da aka tsara,aka raba kungiyoyin shiyyar Asiya guda 20 da matsayi 4 bisa sakamakon da suka samu a gun gasar cin kofin duniya da aka shirya a kasar Jamus a shekarar 2006,daga baya kuma za a zabe su cikin rukuni 5 ta hanyar yin canki-canki.Kunigyar kasar Sin ta halarci bikin bisa matsayi na 2,a gun bikin,mai jagoranci ya sanar da cewa, `Kasar Sin,rukuni na farko.`

Kungiyar kasar Sin tana cikin rukuni na farko wanda ke hada da kungiyoyi masu karfi mafiya yawa.Babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya ta tanadi cewa,kungiyoyi biyu kawai dake cikin wadannan kungiyoyi 20 za su samun iznin shiga gasa ta zagaye na karshe na gasar zagaye na farko da za a shirya a shiyyar Asiya don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta kasar Afirka ta kudu ta shekarar 2010.

Ko tantama kada ka yi,wadannan kungiyoyi uku wato kungiyar kasar Australia da ta kasar Iraki da ta kasar Qatar sun fi karfi a shiyyar Asiya.

Mai tsaron gaba na kungiyar kasar Sin Li Jinyu yana ganin cewa,dukannin kungiyoyi 4 dake cikin rukunin nan suna da karfi sosai,ya ce,  `Ko shakka babu,ana iya kira rukunin da suna `rukunin mutuwa` saboda matsayinsu ya yi kusa kusa,akwai wuya sosai ga kowace kungiya da ta ci nasara,kila ne kungiyar kasar Australia ta fi kadan,gasar dake tsakaninmu ta yi kama da gasa ta matakin karshe.`

Babban malamin koyar da wasa na kungiyar kasar Sin Vladimir Petrovic Pizon yana ganin cewa,idan kungiyar kasar Sin ta yi kokari,to,kila ne za ta ci nasara.`Yan wasan kungiyar kasar Sin su ma suna cike da imani.Mai tsaron tsakiya Zhao Junzhe ya ce,  `Kodayake ana kira rukunin nan da suna `rukunin mutuwa`,amma bai kamata ba ana jin tsoro,idan mun yi kokari,za mu ci nasara kuma matsayinmu zai dada daguwa.`

Daga ran 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2007 zuwa ran 6 ga watan Janairu na shekarar 2008,kungiyar kasar Sin tana yi ta yin aikin share fage domin shiga gasa tsakanin kungiyoyi 20 masu karfi wato suna yin atisaye a jihar Guangdong da jihar Hainan dake kudancin kasar Sin.Daga baya kuma za su tafi kasar hadaddiyar daular Larabawa domin shiga gasar wasan kwallon kafa tsakanin kasashe hudu da za a shirya bisa gayyata.Sa`an nan kuma `yan wasan kasar Sin za su tafi kasar Ingila domin yin atisaye mai tsawon kwanaki 7 a can.Bayan su koma kasar Sin,za su yi nazari kan fasahar wasa ta kungiyar Iraki.

Kodayake kungiyar kasar Sin za ta yi takara da kungiyoyi masu karfi,amma `yan wasan kungiyar kasar Sin suna cike da imani.Muna fatan za su samu sakamako mai gamsarwa. (Jamila Zhou)