Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-19 08:12:51    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (12/12-18/12)

cri

Ran 17 ga wata ne,kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya fayyace cewa,kawo yanzu,yawan hotunan murmushin fuskokin yara da ake tattara domin taya murnar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 ya riga ya kai kusan dubu biyar.Dalilin da ya sa aka shirya wannan aiki shi ne domin kara yin bayani kan kirarin gasar wasannin Olympic ta Beijing wato `duniya daya,buri daya`.Aka fara aikin daga ran 5 ga watan satumba na shekarar 2007 kuma za a kawo karshensa a ran 30 ga watan Afrilu na shekarar 2008.Kila ne za a yi amfani da wadannan hotuna yayin da ake yin nune-nunen wake-wake da raye-raye na bikin bude da rufe gasar Olympic ta Beijing.

Ran 16 ga wata da dare,aka kawo karshen zagaye na karshe na gasar yawon kasa kasa ta babbar kungiyar wasan kwallon tebur ta sana`a ta duniya ta shekarar 2007 wadda aka shafe kwanaki hudu ana yinta bisa sunan `Beijing mai sa`a` a birnin Beijing,`yan wasan kasar Sin sun samu zakarun gasa hudu.A gun zagaye na karshe na gasa tsakanin mata biyu biyu,`yan wasa daga kasar Sin Guo Yue da Li Xiaoxia sun lashe `yan wasa daga kasar Korea ta kudu Kim Kyung Ah da Park Mi Young sun zama zakaru.Daga baya kuma,`dan wasa daga kasar Sin Ma Ling ya samu zama na farko na zagaye na karshe na gasa tsakanin maza,`yar wasa daga kasar Sin Li Xiaoxia ta samu zama na farko na zagaye na karshe na gasa tsakanin mata,ban da wannan kuma,`yan wasa daga kasar Sin Wang Liqin da Chen Qi sun zama zakarun gasa tsakanin maza biyu biyu.

Ran 17 ga wata da asuba,agogon Beijing,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon hannu ta matan duniya ta shekarar 2007 a kasar Faransa,kungiyar kasar Sin ta samu zama na 21,kungiyar kasar Rasha ta zama zakara,kuma za ta shiga gasar kwallon hannu ta gasar Olympic ta Beijing kai tsaye.Kungiyar kasar Norway da ta kasar Jamus sun samu zama na biyu da na uku.An fara gasar ne daga ran 3 ga wata,gaba daya kungiyoyi 24 suka shiga gasar,kuma za a shirya gasar cin kofin duniya ta kwallon hannu ta matan duniya ta shekarar 2009 a kasar Sin.

Ran 14 ga wata,babbar kungiyar wasan kwallon badminton ta duniya ta sanar da sabon jerin sunayen `yan wasan duniya,kungiyar kasar Sin ta samu zama na farko na gasa hudu,wanda a ciki,Lin Dan ya samu zama na farko na gasar maza,Xie Xingfang ta samu zama na farko na gasar mata,Zhang Yawen da Wei Yili sun samu zama na farko na gasa tsakanin mata biyu biyu,Zheng Bo da Gao Ling sun samu zama na farko na gasa ta gaurayen mace da namiji. (Jamila Zhou)