
Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, wannan dakin wasa zai kasance a matsayin cibiyar motsa jiki ga dukkan dalibai da malaman koyarwa na jami'ar ilmin masana'antu ta Beijing, haka kuma za a bude shi ga mazaunan wurin. Bugu da kari kuma, wannan dakin wasa zai ci gaba da kasancewa a wannan kyakkyawar jami'a, a wannan birni a matsayin kayan tarihi na al'adu mai daraja.

Yanzu bari in yi muku bayani kan dakin wasa na karshe na gasar wasannin Olympic da aka gina a cikin jami'o'in Beijing, wato dakin wasa da ke cikin jami'ar ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing, inda za a yi gasanin Judo da Taekwondo a shekara mai zuwa. Akwai kujeru dubu 8 a cikin dakin wasan. Jami'ar ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing wata jami'a ce daban da ta gwanance a fannin ilmin injiniya, shi ya sa masu zayyana suka mai da hankulansu kan tabbatar da amfanin wannan dakin wasa, a maimakon siffarsa ta zamani. An samar da tsarin ba da haske a cikin dakin wasan bisa sabuwar fasaha. Bayan da aka yi amfani da wannan sabuwar fasaha, an shigo da hasken rana domin tabbatar da ba da haske na tsawon awoyi 10 a cikin wannan dakin wasa da rana, sa'an nan kuma, ba a bata albarkatu ko kadan ba. Bugu da kari kuma, hasken rana da ake shigowa ya iya kawar da warin da ke cikin dakin, ta haka za a kiyaye lafiyar mutanen da ke cikin wannan dakin wasa. 1 2
|