Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-17 19:34:27    
An samu babban ci gaba wajen warware matsalar nukiliya ta koriya ta arewa a wannan shekara.

cri

Jama'a assalamu alaikum,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da kuka saba saurara na duniya ina labari.A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani a kan cewa an samu babban cigaba wajen warware matsalar nukiliya ta Koriya ta arewa a wannan shekara. Matsalar nukiliya ta yankin Koriya tana daya daga cikin batutuwan da gamayyar kasashen duniya suka sa lura a kai a shekara ta 2007.Bisa kokarin da bangarorin daban daban suke yi tare,an samu babban cigaba a cikin shawarwari na tsakanin bangarori shida kan batun nukiliya ta Koriya ta arwa.

"Ya kamata Koriya ta arewa ta kammala aikinta na sake tsara fasalin tasoshin nukiliya nata a Yongbyon ta yadda ba za a iya sake amfani da su wajen kera makaman nukiliya ba kafin ran 31 ga watan Disamba na shekara ta 2007.Bisa takardar hadin kai da aka kulla a ran 13 ga watan Fabrairu,Koriya ta arewa ta amince za ta mika cikkakken rahoto na dalla dalla kan shirye shiryenta na makaman nukiliya kafin ran 31 ga watan Disamba na shekara ta 2007.Amurka za ta cika alkwarinta na soke Koriya ta arewa daga jerin sunayen kasashen masu goyon bayan ta'addanci da dakatar da daukar Koriya ta arewa a matsayin kasar makiya wajen yin cinikayya."

Jama'a masu sauraro,abun da kuka ji dazu,shi ne wani kashi ne na takardar hadin kai kan ayyuka a mataki na biyu wajen tabbatar da hadaddiyar sanarwa da mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Wu Dawei ya karanta a bikin rufe tattaunawa ta tsakanin bangarori shida a karo na shida a ran 3 ga watan Oktoba da ya gabata,shi ma shugaban taron tattaunawar nan ne.Sakamako mai amfani da aka samu a cikin wannan tattaunawa yana alamanta cewa tattaunawa ta tsakanin bangarori shida ta samu ainihin sakamako. Kwanan baya yayin da ya yi hira da wakilin gidan rediyonmu, Mr Jun Bong-Geun,shehun malamin cibiyar nazarin harkokin harkokin waje da tsaro a karkashin ma'aikatar harkokin waje da ciniki ta Koriya ta kudu ya darajanta wannan ci gaban da aka samu da cewa "matsalar nukiliya ta Koriya ta arewa,wata matsala ce da wuyan samo bakin zaren warware ta.duk da haka tattaunawa ta tsakanin bangarori shida ta samu ci gaba mai amfani tun farkon shekarar bana. Bangarorin shida sun kulla takardar hadin kai ta ranar 13 ga watan Fabrairu da ta ranar 3 ga watan Oktoba.ko wane bangare ya dauki hakikanan matakai, yunkurin kawar da makaman nukiliya ya samu ainihin ci gaba."

Muhimmin sakamakon da aka samu a wannan mataki na tattaunawa tsakanin bangarori shida kan batun makaman nukiliya ta Koriya ta arewa ba ya iya rabuwa da shawarwarin da aka yi ta hanyoyi daban daban da siffofi iri iri a cikin wannan shekara. A matsayin kasa mai shirya wannan tattaunawa,kullum kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattaunawar gaba.Wannan shehu malami na Koriya ta kudu ya ci gaba da cewa"Duk lokacin da tattaunawa ta tsakanin bangarori shida ta shiga halin kaka-nika-yi, kasar Sin ta kama gaba,ta sanya tattaunawar na cigaba. Kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a cikin tattaunawa tsakanin bangagori shida da za a yi a nan gaba."

Bayan da aka bayar takardar hadin kai ta ranar 3 ga watan Oktoba,nan da nan bangarorin da abin ya shafa sun fara tabbatar da abubuwan da aka tanada a cikin takardar.Koriya ta arewa ta sake tsara fasalin tasoshinta na nukiliya yadda ya kamata,ta kuma samu amaincewa daga kasashen duniya. wani dan tawagar Amurka kan sake tsara fasalin tasoshi Mr Kim Sung ya bayyana cewa "yana da kyau,kuma yana da amfani, mun ziyarci ayyukan nukiliya da ke wurin Yongbyon,ana tafiyar da ayyukan sake tsara fasalin tasoshin yadda ya kamata."

Yayin da wa'adin cika alkawarin da Koriya ta arewa ta dauka na sake tsara fasalin daukacin tasoshinta na nukiliya da gabatar da cikakken rahoto kan shirye shiryenta na makaman nukiliya ya kusanto manam, ko za a iya tabbatar da dukkan abubuwan da aka tanada a cikin takardar hadin kai ta ranar 3 ga watan Oktoba daga dukkan fannoni kuma cikin lokaci ya zama batun da ya fi jawo hankulan mutane. A ganin Mr Jin Dexi,mataimakin shugaban ofishin bitar harkokin Japan na cibiyar nazarin harkokin zamantakewa da ilimi ta kasar Sin,da wuyan a cimma burin da aka sanya gaba na kammala ayyukan sake tsara fasalin tasoshin da bayar da shirye shiryenta na makaman nukiliya kafin karshen shekarar nan.Mr Jin Dexi ya ce"Matsalolin da aka samu a yanzu sun shafi fasaha.Alal misali, a ganin bangarorin da abin ya shafa,sake tsara fasalin tasoshin,aiki ne na saukakke.a hakika ayyukan sake tsara fasali na bukatar lokuta da kudade. Na biyu,da akwai rashin amincewar juna da ya dade kasancewa tsakanin Amurka da Koriya ta arewa, da wuyan a soke shi rana daya.shi ma na bukatar lokaci."

Mr Jin Dexi ya yi nuni da cewa, kamata ya yi a dauki yunkurin da ake yi na warware matsalar makaman nukiliya ta Koriya ta arewa a matsayi yadda ya kamata.Idan a yi la'kari da nan gaba,tabban ne za a iya kawar da makaman nukiliya daga yankin Koriya,amma ba za a iya gudanar da yunkurin tare da sauki ba.

Jama'a masu sauraro,wannan dai ya kawo karshen shirinmu na yau na duniya ina labari.Mun gode muku saboda kun saurarenmu.(Ali)