Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-17 16:46:30    
Yanzu kuma za mu kawo muku wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

cri

---- A ran 24 ga watan Nuwamba a nan birnin Beijing an bude nunin nasarorin da aka samu wajen ayyukan harsuna da babbakun kananan kabilun kasar Sin wanda kwamitin harkokin kabilun kasar Sin da ma'aikatar ba da ilmi ta kasar suka shirya ta hanyar hadin gwiwa.

A gun nunin, an nuna nasarorin da kasar Sin ta samu tun bayan kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin zuwa yanzu wajen buga labaru da watsa labaru da sinima da talebijin da fassara cikin daidaituwa, da aikin sadarwa da yin gyare-gyaren tittattafan tarihi da rubuce-rubuce ta hanyar yin amfani da harsuna da babbakun kananan kabilun kasar.

---- A ran 22 ga watan Nuwamba a nan birnin Beijing, an yi babban taron murnar ranar cika shekaru 20 da kafa babban kolejin koyon addinin kabilar Tibet. Madam Liu Yandong, mataimakiyar shugabar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya halarci babban taro kuma ta ba da jawabi a gun taron.

Madam Liu ta bayyana cewa, cikin shekaru 20 da suka wuce, babban kolejin koyon addinin kabilar Tibet kullum yana tsayawa haikan ga bin manufa da ka'ida masu gaskiya wajen ba da ilmi, kuma ya tallafa wasu kwararrun mutane a fannin addinin kabilar Tibet, ya ba da babban taimako domin kara karfin masu kishin kasa na sassan addinin kabilar Tibet da samun ci gaba mai dorewa a jihar Tibet da sauran wuraren da 'yan kabilar Tibet ke zama.

---- A ran 25 ga watan Nuwamba a gundumar Gongcheng ta kabilar Yao mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta lardin Guangxi da ke kudancin kasar Sin, an yi bikin Panwang wato bikin yin addu'a domin tunawa da kakanninsu a karo na 9 na kabilar Yao ta kasar cikin gagarumin hali.

Bisa labarin da aka bayar an ce, da akwai wasu gundumomin kananan kabilu na lardunan Guangxi da Guangdong da Hunan da Yunnan wadanda suka aika da kungiyoyin wakilansu domin halartar wannan taro, ban da wannan kuma kungiyoyin 'yan kabilar Yao na kasar Vietnam da na sauran kasashen ketare su ma sun aika da wakilansu don halarci wannan taro bisa gayyatar da aka yi musu. Ayyukan da aka yi a gun wannan babban biki suna kunshe da bikin yin addu'a domin tunawa da kakanninsu, da yin taron kara wa juna sani kan ilmin kabilar Yao, da yin wake-wake da raye-raye na kabilar, da yin yawo domin kallon abubuwan halittu masu rai, da kuma yin nuni da sayar da 'ya'yan itatuwa.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)