Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-14 15:34:31    
Amsoshin tambayoyi a kan gasar kacici-kacici dangane da wasannin Olympics na Beijing

cri
A yanzu haka dai, mun riga mun fara gasarmu ta kacici-kacici dangane da wasannin Olympics na Beijing. To, amma dai, a kwanan nan, mun sami tambayoyi da yawa daga wajen masu sauraronmu dangane da gasar.

Malam Shuaibu Muhammed Rijiyar maikabi, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Kamba, Jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, ga shi kun fara gudanar da gasar kacici kacici ta wannan shekara, to ga shi kuma ba ku fara manna gasar ba ta duniyar Gizo dinku, shin ko ba mu ba da amsa ba har lokacin da kuka fara saka ta, ta duniyar gizon dinku.

Sai kuma Musa Tijjani ya yi mana tambaya cewa, ina bukatar karin bayani game da gasar, shin tambayoyi shida zan amsa cikin takwas? ko kuna nufin in amsa takwas in na ci shida na shiga gasar.

Akwai kuma Hauwa Isah, da ta fito daga akwanga, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, wadda ta rubuto mana cewa, mako biyu da su ka wuce, da kuma makon da ya gabata na saurari bayani game da gasar amma bayanin kadan ne. A shafinku kuma babu bayanai sosai ta yadda zamu samu amsar gasar.

Ban da su, akwai kuma malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin birnin Keffi da ke jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, yau da gobe sai ALLAH gashi dai ya rage kasa da shekara guda a gudanar da wasannin olympic na shekara ta dubu biyu da takwas a birnin Beijing.Yanzu dai ku sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin kun soma gudanar da gasar kacici kacici sai dai ni Sanusi Isah Dankaba akwai wani tsokaci da nike so in yi dangane da ambulan da kuke aiko mana dashi dauke da tambayoyin gasar kacici kacici, shin abun tambaya a nan ko wannan shekara za ku aiko mana da wannan ambulan ko a'a.Yanzu dai dobara ta rage ma mai shiga rijiya, ni dai zan aiko da amsoshin wannan gasar kacici kacici ta "mu hadu a shekara ta dubu biyu da takwas" kai tsaye ta hanyar email, kuma zai yi amfani da ambula idan harma kun ba mu shi, kuma amsata za ta kasance iri guda.

To, domin amsa tambayoyin wadannan masu sauraronmu, yanzu bari in kawo muku karin bayani a kan gasar. Kamar yadda kuka sani cewa, za a gudanar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi a karo na 29 daga ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedwatar kasar Sin. Domin kara fadakar da masu sauraronmu a kan gasar, tun daga ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, gidan rediyon kasar Sin ya kaddamar da wata gasar ka-cici-ka-cici mai ban sha'awa a game da wasannin Olympics na Beijing, wadda ke da lakabin 'Mu hadu A Shekarar 2008', kuma za mu kawo karshen gasar a ran 1 ga watan Mayu na shekara mai kamawa. A lokacin gasar kuma, za mu gabatar muku da shirye-shiryen musamman guda hudu game da wasannin Olympics na Beijing daya bayan daya. Sa'an nan, a karshen kowane shirin musamman, za mu kawo muku tambayoyi guda biyu game da gasar, wato gaba daya za ku amsa tambayoyi guda takwas ke nan a cikin gasar. Sa'an nan kuma, yanzu mun riga mun fara manna bayanai hudu na gasar a kai a kai a shafinmu na internet, yanzu kuna iya karanta bayanan daga shafinmu na internet, kuma a filinmu na wasannin Olimpics na Beijing, wanda ke tsakiyar shafin. Daga karshe kuma, a game da hanyoyin amsa tambayoyin gasar, to, masu sauraro, ba da jimawa ba, za mu aika muku da ambulan da ke dauke da tambayoyinmu, sa'an nan, kuna iya turo mana amsoshinku cikin ambulan zuwa akwatin gidan wayarmu, kuma akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya shi ne, China Radio International P.O.Box 72100, Victoria Island, Lagos Nijeriya, kuma a nan kasar Sin akwatin shi ne Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040, kuna kuma iya aiko mana Email kai tsaye a kan Hausa @cri.com.cn. Masu sauraro, muna fatan za ku yi kokarin shiga gasar, kuma duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman cikin wannan gasa za su iya samun damar kawo ziyara a nan birnin Beijing a watan Yuni na shekara mai zuwa da kuma shiga bukukuwa masu kayatarwa da abin ya shafa. Sai mu hadu a nan birnin Beijing.