Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-14 15:32:30    
Gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya da CRI ta gudanar a game da taron wasannin Olympics na Beijing(babi na uku)

cri
Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuke sanin cewa, za a gudanar da taron wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 tsakanin ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Domin samar muku da wata kyakkyawar damar kara samun ilmi da kuma sa hannu cikin harkokin taron wasannin, tun daga yau wato ran 9 ga watan da muke ciki, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya kaddamar da gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya a game da ilmin taron wasannin Olympics na Beijing, wadda ke da lakabi haka: " Mu yi haduwa a shekarar 2008" ta hanyar yin amfani da harsunan waje 38, da Sinanci, kare-karen harsuna iri 4 na wuraren kasar Sin da kuma tashar internet wato www. cri.com.cn.

Gasar nan za ta dauki rabin shekara. A cikin wannan lokaci dai, za mu watsa bayanan musamman guda 4 na game da taron wasannin Olympic daya bayan daya; kuma a karshen kowane bayanin musamman, akwai tambayoyi guda biyu game da taron wasannin. To, za ku iya shiga wannan gasa ta hanyar sauraron shirye-shiryenmu. Abin da ya fi burge aminai masu sauraronmu shi ne, duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman, za su iya kawo ziyara nan Beijing a watan Yuni na shekara mai zuwa.

Aminai masu sauraronmu, kamar yadda kuke sanin cewa, yanzu lokaci bai kai shekara guda ba da ya rage a gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing. A bisa matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan share fagen gasar wasannin, ayyukan gina filaye da dakunan wasanni suna tafiya kamar yadda ya kamata.

Filaye da dakunan wasanni guda 37 ne za a yi amfani da su domin wannan gagarumar gasa; kuma guda 19 sabbabi ne daga cikinsu tare da gyaran guda 11 da kuma gina guda 7 na wucin gadi, wadanda aka zuba jari da yawansu ya kai kimanin dalar Amurka biliyan biyu da miliyan dari shida da saba'in wajen gina su. Gwamnatin kasar Sin da ta birnin Beijing na mai da hankali sosai kan aikin gina wadannan filaye da dakunan wasa.

Ana kiran babban filin wasan motsa jiki na kasar Sin " Gidan tsuntsaye" wato " Bird's Nest" a Turance, inda za a gudanar da bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 da kuma bikin rufe ta. An soma gina wannan filin wasanni ne a watan 12 na shekarar 2003. Mataimakin injiniya mai kula da aikin gina shi Mr. Li Jiulin ya furta cewa: " Wani muhimmin halin musamman ne aikin gina wannan filin wasa mai siffar gidan tsuntsaye shi ne, ana yin afmani da sabbin fasahohi da kuma kayayyaki wajen gina shi. Ana sa ran cewa, wannan filin wasa zai kasance wani gini mai kayatarwa dake alamanta surar birnin Beijing, wanda kuma zai janyo hankulan jama'ar duniya a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing."

Jama'a masu sauraro, wani gini daban dake kusa da filin wasanni mai siffar gidan tsuntsaye shi ne cibiyar wasan iyo ta kasar Sin. Ana kiranta "Tafkin wanka" wato " Water Cube" a takaice, inda za a gudanar da gasannin iyo, da na tsunduma cikin ruwa da kuma na kwallon ruwa wato water polo.

A lokacin da aka fasalta ginin cibiyar wasan iyo ta kasar tun da farko, masu zayyana shirin gina shi sun yi namijin kokari wajen tabbatar da hasashen " Ruwa" ta hanyar bayyana " sinadarin ruwa" da kuma "siffar gini mai kusurwa 4 na ruwa" wato "water cube". Daga nan dai, mai fasalin ginin daga bangaren kasar Sin Mr.

Ban da wannan kuma, ana tabbatar da hasashen " gudanar da gasar wasannin Olympics cikin kyakkyawan muhalli" da na " kimiyya da fasaha" a lokacin da ake gina filaye da dakunan wasannin, musamman ma na tseren kwale-kwale a birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin. Ministan ayyuka da kiyaye muhalli na kwamitin tseren kwale-kwale na Qingdao, Mr.Li Zhipeng ya bayyana cewa: " Mun yi amfani da fasahohi da kuma kayyayaki na zamani wajen gina cibiyar tsare-tseren kwale-kwale da zummar bada misalai ga zamantakewar al'ummar kasar, ta yadda za a kara yin farfaganda kan hasashen 'gudanar da wasannin Olympics cikin kyakkyawan muhalli'".

Jama'a masu sauraro, tun bayan da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya danka wa birnin Beijing nauyin gudanar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi na shekarar 2008 a ran 13 ga watan Yuli na shekarar 2001, gwamnatin birnin Beijing ta tsara cikakkun shirye-shiryen share fagen gasar wasannin, har ta samu sakamako mai gamsarwa. Babban jamirin kwamitin wasannin Olympics na duniya Mr.Hain Verbruggen ya jinjina wa gwamnatin birnin Beijing, cewa: " Ina farin ciki matuka da fadin cewa, ana gina filaye da dakunan wasa na gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin hanzari kuma daidai bisa shirin da aka tsara. Hakan ya sosa raina kwarai da gaske".

To, aminai masu sauraronmu, kafin mu kawo karshen bayanin musamman na yau, barin in kawo muku tambayoyi guda biyu dake shafar bayanin. Tambaya ta farko ita ce : Filaye da dakunan wasa nawa ne za a yi amfani da su domin gasar wasannin Olympics ta Beijing ? Tambaya ta biyu ita ce : Mene ne sunan filin wasa na kasar Sin, inda za a gudanar da bikin bude wannan gagarumar gasa da kuma bikin rufe ta ?

A mako mai zuwa, za mu kawo muku bayanin musamman na hudu wato na karshe a game da wannan gasar wasanni, wanda ke da lakabi kamar haka: " Bayani kan biranen da suka bada taimako wajen gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing '' . ( Sani Wang )