Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-13 15:40:41    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin(11)

cri
----An kama wani mutum da ya yi cinikayyar koyaton wata dabba.A filin jiragen sama na Xianyan na dab da birnin Xi'an na lardin Shaanxi na kasar Sin,ma'aikata masu tsaro a filin sun tsare wani mutum da ya ke shiga wani jirgin sama zuwa birnin Shanghaim,yayin da ma'aikatan tsaro binciken kayayyaki,an gano wani koyaton dabbar a cikin kunshinsa wanda aka hana tafiyar da shi a fadin kasa domin kare dabbobi da muhalli.koyatonsa dabbar magani ne mai gina jiki bisa likitancin gargajiya na kasar Sin,shi ya sa a kan samu wasu mutane na farautar dabbobi domin samun koyatonsa da yin cinikayyarsu. Da aka kama mutumin nan sai aka yi masa tara mai dimbin yawa.

----'Yan makaranta sun shirya wasannin Olympics.Dalibai kimanin dubu 15 daga wata makaranta a yankin yammacin birnin Beijing sun shirya wani bikin fara wasannin Olympics a harabar makarantarsu duk domin kara saninsu kan 'yan wasa na kasashe daban daban na duniya. An tsara dalibai cikin kungiyoyi 39 na 'yan wasa na kasashen ketare da suka shiga kaya irin nasu na gargajiya suka yi maci suna kuwwa suka gaida 'yan kallo. 'yan makaranta sun yi magana da harsuna daban daban.Sun yi wannan bikin ne a ranar lahadin da suka yi hutu.Wani malami a wannan makaranta ya ce makasudin shirya wannan bikin wasannin Olympics shi ne domin kara sanin 'yan makaranta kan wasannin Olympics da al'adu da dabi'u na sauran kasashen duniya.

----Binciken lafiyar jiki ya zama wani aikin jama'a a ranaikun hutu a kasar Sin.Ma'aikatan hukuma na birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin sun taru a cikin asibitoci bayan ranaikun hutu na bikin kasa duk domin bincike lafiyarsu,wannan ya riga ya zama sabon yayi a kasar Sin. Wannan ba bakon abu ba ne ga mutanen birane da suka yi amfani da ranaikun hutu da warkar da cututtukan da suke fama da su cikin dogon lokaci kamar su ciwon tumbi da ciwon gabobi.Yanzu mutane masu tarin yawa sun gane muhimmancin lafiya kamar yadda Hausawa suke fada"lafiya uwar jiki ne "saboda matsin lamba na tsananin gajiya da suka kamu da ita..Wani likita ya ce da ya ke mun sha aiki a ranaikun hutu, mun yi farin ciki da ganin mutanen da suka taru a asibitoci domin binciken lafiyarsu,wannan yana shaida cewa ma'aikatan hukuman da suka sha aiki a ofisoshin sun fara dora muhimmanci kan lafiyarsu.

----Wani tsoho da ya kan ceci mutane daga ruwa yana alfahari da yin taimako.Wani tsoho mai yawan shekaru 65 da haihuwa da ake kiransa Zhao Yuanzhang ya ceci wani mutum da ya nutse cikin ruwan kogi a ranar lahadi da ta gabata. Wannan ba bakon abu ba ne gare shi. Shi direba ne daga birnin Changchun na lardin Jilin na arewa maso gabashin kasar Sin.Tsohon nan ya ce "na yi abin da ya kamata in yi ne. "Yaya zan yi na taimaki wanda rayuwarsa take cikin hadari?Na saba da taimakon mutanen da suka sha wahala." A cikin yan shekarun baya,tsohon nan ya ceci mutane da dama da suka nutse cikin ruwan kogi.Wani ma'aikacin hukuma na lardin Jilin mai suna Dong ya ce yana so ya kafa wani asusu domin yaba wadanda suka yi abin kirki. A ganinsa tsohon nan ya cancanci samun lakabin gwarzo da abin misalin koyo ga sauran mutanen kasa.

---'Yan sanda sun ba da taimako ga makafi. 'Yan sanda na birnin Fuxin na lardin Liaoning na kasar Sin suna taimakon makafi 20 cikin shekaru 22 da suka gabata wajen kula da zamansu na yau da kullum.Wadannan 'yan sanda sun zo ne daga wani ofishinsu dake dab da gidan makafi wanda suka yi ritaya daga ayyukanku.Bayan da suka tashi daga aiki,'yan sanda su kan je gidan makafi da yamma,su tsabtace gidan makafi da kwashe shara da sauran ayyuka a gida,wani lokaci ma sun zagaya waje da gida domin kawar da katanga da ke wajen wurin gidan domin samar da saukin tafiya ga makafi.Har ma sun girka alamun da makafi suka iya amfani da su wajen yin tafiya.

----An samar da ilimi ga matasa wajen inganta mu'amala dake tsakaninsu. A lokacin hutu na bikin kasa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin a kan koya darussa ga matasa masu aiki a ofis dangane da inganta mu'amala tsakanin mata da maza.Wadanda suka shiga kos na samar da ilimi,yawancinsu ma'aikata ne da ke aiki a ofis domin aiki ya kan yi musu yawa har ma ba su da lokacin samun abokan zama.shi ya sa sassan da abin ya shafa suka shirya kos inda aka samar da ilimi kan matasa da koya musu waka da rawa da kuma ka'idojin da ake bi wajen yin mu'amala tsakanin mata da maza,ta haka kuwa za su kara kwarewarsu kan yin mu'amala da sauran matasa.

---An kama wani mutum da ake tuhumarsa da satar kudi. An kama wani mutum mai suna Bau a yankin mulkin musamman na Hongkong na kasar Sin sabo da ya yi nufin satar kudi.Yayin da mutumin nan ya shiga layi ya shiga burtun daukar kudi daga wata na'uar da ake kira ATM,wani mutum dake gabansa ya yi amfani da na'urar amma bai dauki kudin tsabar,sai ya fita daga layi,jin kadan ya sake shiga layi.Da wani mutum daban dake gabansa ya yi amfani da na'uar wajen daukar kudi,mutumin nan ya yi wayar salula yayin da yake amfani da na'uar,har ma ya yi wauta ya manta tsabar kudin da na'urar ta fitar.A wannan lokacin mutumin da muka ambata sama ya kama gaba ya tafi da kudin.Daga bisa aka gane ainihin labari saboda bidiyon da aka dauka ya tanadi duk labarin kan abin da ya yi.An kama mutumin nan da ya dauki kudi ba nasa ba.(Ali)