Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-13 14:55:50    
Kasar Sin tana kokarin rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi domin yaki da sauyin yanayi

cri

A ran 12 ga wata an shiga zagaye na matakin koli a babban taron M.D.D. kan muhalli da ke gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesia, wakilan da abin ya shafa da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 180 sun yi shawara kuma sun tatauna matsalar cimma daidaito kan butun rage yawan gurbatacciyar iskar da ke dumama yanayi bayan shekarar 2010. A gun taron manema labarun da aka yi bayan taron, Mr. Xie zhenhua, mataimakin direktan kwamitin bunkasuwa da yin gyare-gyaren kasar Sin, kuma shugaban kungiyar wakilan kasa ya amsa tambayoyin da 'yan jaridu suka yi masa kan wannan batu. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayanin da wakilinmu ya ruraito mana kan wannan labari.

Lokacin da ake tattaunawa kan batun kafa tsarin yin shawarwari, kasashe masu tasowa sun tsaya kan matsayinsu wajen gudanar da "tsarin hanyoyi 2" wato hanya ta farko ita ce, a kafa kungiyar musamman bisa "Yarjejeniyar Kyoto" don tattauna alhaki da kasashe masu sukuni suka dauka wajen rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi a mataki na 2 na yin alkawarin cimma daidaito. Hanya ta 2 kuma ita ce, a sa kaimi ga kasar Amurka wadda ba ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ba da ta shiga shawarwarin. Amma wasu kasashe sun gabatar da cewa suna son yin shawarwari ta hanyar hada wadannan hanyoyi 2. Mr. Xie ya bayyana kan wannan butu cewa. "Hakikanin sakamakon hada wadannan hanyoyi 2 shi ne, shigar da kasashen Amurka da Sin da Indiya da sauran wasu muhimman kasashe masu tasowa cikin jerin kasashe masu rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi bisa ma'auni iri daya, ba za mu yarda ba wannan ra'ayi ba ko kusa domin babu gaskiya a cikin sa."

A gun taron, kungiyar wakilan kasar Sin ta yi shawarwari tsakanin gefuna 2 wato a tsakaninta da kasashe fiye da 30, kuma ta rubanya kokari don yin shawarwari tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samu ra'ayi daya tsakanin bangarori daban-daban tun da wuri kan matsalar rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi. Mr. Xie ya ce, "Ina jin cewa, shawarwari da muke yi suna da amfani sosai. Ya zuwa yanzu, mun riga mun bayyana ra'ayoyinmu tare da wakilan wasu kasashe masu tasowa. Dukkan ra'ayoyin da muka dauka kan ajandar taron da manufofin da za mu tabbatar da su da kuma matakan da za mu dauka daya ne."

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar sin dauki matakai masu yakini wajen rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi domin yaki da sauyin yanayi, kuma ta samu nasarori a bayyane. Mr. Xie ya bayyana cewa, "Alal misali, cikin shekaru 15 da suka wuce wato daga shekarar 1990 zuwa ta 2005, yawan makamashin da kasar Sin ta aiwatar da su wajen bunkasa tattalin arziki ya ragu da da kashi 47 bisa 100, wato ya ragu da fid da gurbataccen hayaki da ake kira carbon dioxide Ton biliyan 1.8. Ban da wannan kuma muna nan muna kokarin daukar matakai daga sauran fannoni, alal misami muna aikin bukasar makamashin bola jari wato makamashin da za a iya sake yin amfani da su, yawan kudin da muka ware a shekarar 2007 kawai ya wuce dala miliyan 20 a dukkan al'umman kasar Sin domin bunkasa makamashin da za a iya sake yin amfani da su."  (Umaru)