Yau 12 ga wata, an shirya gaggarumin taro a babban dakin taron jama'a na birnin Beijing don murnar cikakkiyar nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin aikin binciken wata a karo na farko. Mr Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar ya halarci taron inda ya bayar da jawabi mai muhimmanci cewa, nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin aikin binciken wata a karo na farko ta nuna cewa, kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin kasashen duniya wadanda ke iya binciken samarin samaniya, kuma ta zama sabon sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yin kirkire-kirkire cikin cin gashin kai da raya kasa ta sabon salo. Bayan haka ya jaddada cewa, kasar Sin tana binciken sararin samaniya ne domin cim ma manufar zaman lafiya.
Yau ana cike da annashuwa a cikin takafarin babban dakin taron jama'a na birnin Beijing. Mr Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da sauran shugabannin jam'iyyar da na kasa da wakilan masu binciken wata da kuma wakilan bangarorin birnin Beijing daban daban wadanda yawansu ya wuce 5000 sun halarci taron don yin kyakkyawar murnar cikakkiyar nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin aikin binciken wata a karo na farko. A gun taron, Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, "nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin aikin binciken wata a karo na farko ta zama babban ci gaban da ta samu wajen bunkasa harkokin binciken sararin samaniya, bayan da ta samu nasara wajen haraba tauraron dan adam da kumbo mai dauke da dan sama-jannati, kuma ta zama wata ishara cewa, kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin kasashen duniya wadanda ke iya binciken sararin samaniya. Haka kuma wannan babban taimako ne da jama'ar kasar Sin suka bayar wajen yin amfani da sararin samaniya domin tabbatar da zaman lafiyar dan adam."
Wannan nasara kuma ta aza harsashi mai inganci ga zurfafa binciken da kasar Sin ke yi kan sararin samaniya, kuma ta sa jama'ar kasar Sin su kara nuna kishin kasar. Mr Hu Jintao ya nuna cewa, "nasarar da kasarmu ta samu wajen yin aikin binciken wata a karo na farko ta kara nuna cewa, kasarmu ta kara sami karfi a fannin tattalin arziki, da kimiyya da fasaha da inganta hadin kan jama'ar kasa, da kara ba da gwarin gwiwa ga duk jama'ar kasar Sin da su nuna kishin kasa, kuma ta kara karfafa wa jama'ar duk kabilun kasar Sin zuciya da aniyarsu wajen raya zamantakewar al'amma mai wadata daidai gwargwado da gaggauta raya zaman gurguzu na zamani."
Aikin binciken wata da kasar Sin ta yi a karo na farko matakin farko ne da ta dauka wajen binciken sararin samaniya. Mr Hu Jintao ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su ci gaba da yin aikin bincikensu da kayu, su cim ma babbar manufar binciken wata. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na binciken sararin samaniya ne duk bisa manufar zaman lafiya. Ya kara da cewa, "amfani da sararin samaniya cikin lumana sha'ani daya ne ga bil adamu, kuma yana dacewa da moriyar bil adamu baki daya. Jama'ar kasar Sin tana son hadin kanta da jama'ar kasashe daban daban, su nace ga bin manufar gaskiya game da yin amfani da sararin samaniya cikin lumana, ta nuna himma ga yin hadin kan kasa da kasa don binciken sararin samaniya. Kuma za ta ci gaba da neman samun babban ci gaba wajen binciken sararin samaniya, ta yi kokai wajen kara ba da babban taimakonta don sa kaimi ga ciyar da kimiyya da fasaha ta dan adam gaba, da sa kaimi ga yalwata babban sha'anin zaman lafiya da samun bunkasuwa domin dan adam." (Halilu)
|