Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-12 11:21:33    
Aikin share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ya shiga sabon mataki na gwaji da kyautatuwa da na kammalawa

cri
Ran 11 ga wata, a nan Beijing, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, yanzu aikin share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ya shiga sabon mataki na gwaji da kyautatuwa da kuma na kammaluwa.

A wannan rana, ta hanyar wayar tarho ta talibijin, Mr. Liu Qi ya yi bayani kan ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ga taron kwamitin gudanarwa na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da ake yi a birnin Lausanne na kasar Switzerland.

Mr. Liu ya kara da cewa, tun daga farkon wannan shekara har zuwa yanzu, ingancin iskar Beijing ya ci gaba da samun kyautatuwa. Yawancin filayen wasa da na aikin horo da gine-ginen da abin ya shafa sun kawo karshen ginawa da kuma samun kwaskwarima bisa shirin da aka tsara, sun kuma ci jarrabawa ta hanyar yin gasar 'Good Luck Beijing', a galibi dai, sun biya bukatun shirya gasar wasannin Olympic.

Ya ci gaba da cewa, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing zai ci gaba da tuntubar kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa wajen gudanar da rarraba tikiti yadda ya kamata.(Tasallah)