Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-11 09:34:50    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(06/12-12/12)

cri
Ran 7 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, Ran Chengqi, mataimakin darektan cibiyar kula da ayyukan jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam ta kasar Sin ya bayyana cewa, tsarin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adama mai suna 'Beidou' da kasar Sin ta mallaki ikon mallakar ilmi da kanta zai ba da hidima wajen jagorancin zirga-zirga da kuma sa ido kan tsaron filayen wasa domin gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekara mai zuwa. Wannan jami'in kasar Sin ya kara da cewa, cibiyar da kwamitin kula da harkokin zirga-zirga na birnin Beijing sun yi hadin gwiwa a tsakaninsu, sun riga sun iya tabbatar da ganin injin jagorancin zirga-zirga da aka ajiye a cikin mota, sun kuma yi amfani da tsarin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam mai suna 'Beidou' wanda ke iya nuna halin da Beijing yake ciki a fannin zriga-zirga cikin lokaci.

Ran 6 ga wata, a nan Beijing, a hukunce ne mai shirya taron baje-koli na wasan Olympic a karo na farko ya gayyaci duk duniya da su shiga taron baje-kolin. Kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma kwamitin wasan Olympic na kasar Sin suka shirya wannan taron baje-koli kafada da kafada, sa'an nan kuma, kamfanin gidan waya na kasar Sin shi ne ya dauki bakuncin taron baje-kolin. Za a bude wannan taron baje-koli a dakin nune-nune na Beijing tun daga ran 8 zuwa ran 18 ga watan Agusta a shekara mai zuwa. Taron baje-kolin zai shafi kan sarki na wasan Olympic da tambari da tsabar kudi da kayayyakin fasaha. Bugu da kari kuma, a gun taron baje-kolin, za a nuna da kuma sayar da kan sarki da suka fito daga kasa da kasa da kayayyakin da abokan kwamitin wasan Olympic na duniya a fannin yin hadin gwiwa da abokan kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma masu ba da kudade domin gasar wasannin Olympic ta Beijing suka shirya.

Ran 5 ga wata, a birnin Lausanne na kasar Switzerland, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta kasa da kasa ta gabatar da sabon jerin 'yan wasan kasa da kasa. 'Yan wasan kasar Sin sun zama na farko a tsakanin 'yan wasan kwallon tebur a tsakanin najimi da najimi da kuma a tsakanin mace da mace.

Ran 9 ga wata, a nan Beijing, an rufe gasar cin kofin duniya ta tseren keke a filin wasa ta 'Good Luck Beijing ' mai tsawon kwanaki 3. Kungiyar kasar Netherlands ta zama ta farko a cikin jerin kasashe masu halartar gasar saboda samun lambobin zinariya 4 da na tagulla 2, kasar Sin kuwa ta sami lambobin tagulla 2. A ciki kuma, dan wasa Li Wenhao ya zama ta uku a cikin gasar tseren keke mai tsawon kilomita 1 a tsakanin maza bisa gwajin lokaci, sa'an nan kuma, kungiyar kasar Sin ta sami lambar tagulla a cikin gasar tseren keke a tsakanin kungiya-kungiya ta mata bisa gwajin sauri. An bude wannan gasa a ran 7 ga wata, inda 'yan wasan tseren keke fiye da 390 daga kasashe da yankuna 47 suka kara da juna a cikin kananan shirye-shirye 17.(Tasallah)