Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-10 17:02:58    
Kasar Sin ta sami kyakkyawan sakamako wajen yin amfani da sahihiyar manhaja

cri

Ran 10 ga wata, Malam Liu Binjie, babban darekatan hukumar kula da hakkin mallakar fasahar dabi ta kasar Sin ya bayyana a gun wani taron da aka shirya a birnin Beijing cewa, yanzu, kasar Sin tana kokari sosai wajen sa kaimi ga yin amfani da sahihiyar manhaja, kuma ta riga ta sami kyakkyawan sakamako. Ya ce, wannan matakin da kasar Sin ta dauka ya samar da kyakkyawar manufa game da sa kaimi kan bunkasa harkokin manhaja a kasar yadda ya kamata.

An shirya taron kasar Sin kan ayyukan yin amfani da sahihiyar manhajja a ran 10 ga wata a nan birnin Beijing. Shugabannin hukumar kula da hakkin mallakar fasahar dabi da na ma'aikatar sadarwa da ta kasuwanci da kudi da kuma jami'an hukumomin wurare daban daban na kasar da wakilan kamfanoni da sana'o'i da abin ya shafa wadanda yawansu ya kai kimanin 300 sun halarci taron. Malam Liu Binjie, babban darektan hukumar kula da hakkin mallakar fasahar dabi ta kasar ya bayar da jawabi a gun taron cewa, yanzu, hukumomin gwamnatocin larduna da jihohi da manyan birane da ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar kai tsaye na babban yankin kasar Sin wadanda yawansu ya kai 31, da kuma kananan hukumomi sama da 300 na wurare daban daban dukanninsu sun riga sun cim ma manufar yin amfani da sahihiyar manhaja kafin karshen shekarar bara, sa'an nan kamfanoni da masana'antu su ma sun sami kyakkyawan sakamako wajen yin amfani da sahihiyar manhaja. Malam Liu ya ce, "bisa kokarin da gwamnatocin matakai daban daban da hukumomin kula da sana'o'i iri-iri suka yi tare, yanzu, manyan masana'antu kimanin 1500 na kasar sun riga sun kammala aikinsu na yin amfani da sahihiyar manhaja. Haka kuma akwai masana'antu sama da 1300 wadanda aka kamalla aikin yin amfani da sahihiyar manhaja, an sami kyakkyawan sakamako wajen sa kaimi ga masana'antu da su yi amfani da sahihiyar manhaja a cikin wani lokaci."

Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun daga shekarar 2002, hukumomin gwamnatin kasar Sin sun shafe shekaru uku suna gudanar da harkokin yin amfani da sahihiyar manhaja, haka kuma hukumomin gwamnati na jihohi da wurare su ma sun kammla aikin yin amfani da sahihiyar manhaja, sun gwada kyakkyawan misali ga duk zamantakewar al'umma da su yi amfani da sahihiyar manhaja.

Yayin da Malam Wang Ziqiang, shugaban sashen hakkin mawallafi na hukumar kula da hakkin mallakar fasahar dabi ta kasar Sin ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi kokari sosai wajen sa kaimi ga yin amfani da sahihiyar manhaja, wanda ba safai a kan ga irinsa ba a duniya. Ya kara da cewa, "gwamnatin kasar Sin tana amfani da albarkatunsa da na jama'a wajen sa kaimi ga yin amfani da sahihiyar manhaja don kiyaye ikon mallakar ilmi. Wannan ba safai a kan ga irinsa ba a kasashe daban daban. Sa'an nan ya nuna ra'ayi da niyyar da gwamnatin kasar Sin ta nuna don kiyaye ikon mallakar ilmi."

Sana'ar yin manhaja tana da muhimmanci sosai ga sana'ar sadarwa, kuma ga tattalin arzikin kasa da zaman jama'a. Tun da aka shiga sabon karni, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai ga bunkasa sana'ar yin manhaja ta kasar, ta tsara wasu manufofin sa kaimi ga bunkasa sana'ar yin manhaja, kuma ya bukaci duk zamantakewar al'umma ta yi amfani da sahihiyar manhaja. Sa'an nan kuma tun daga shekarar 2006 zuwa ta 2007, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai musamman domin yaki da manhajar jabu da ake amfani a cikin na'urori masu aiki da kwakwalwa a kasar.

Amma Malam Liu Binjie, babban daraktan hukumar kula da hakkin mallakar fasahar dabi ta kasar Sin ya bayyana cewa, sa kaimi ga yin amfani da sahihiyar manhaja wani aiki ne mai nauyi da ake yi har cikin dogon lokaci. Bisa shirinsa, gwamnatin kasar Sin za ta shafe shekaru biyar tana yin kokari wajen tabbatar da duk masana'antun kasar da su yi amfani da sahihiyar manhaja. (Halilu)