Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-10 15:54:49    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Kwanan baya yayin da Mr. Hao Peng, mataimakin shugaban kula da harkokin yau da kullum na jihar Tibet mai zaman kanta ta kasar Sin yake binciken halin da ake ciki a farkon watanni 9 na wannan shekara wajen tattalin arziki ya bayyana cewa, sabo da an mai da muhimmanci sosai kan zaman rayuwar jama'a na jihar Tibet, ta samu tabbaci ga zaman rayuwar jama'a masu fama da talauci daga fannoni da yawa, shi ya sa jama'a sun kara samun kyautatuwa wajen zaman jin dadinsu.

Ya zuwa karshen watan Satumba na wannan shekara, manoma da makiyaya dubu 230 wadanda matsakaicin yawan kudin shiga da suka samu ba su wuce kudin Sin wato Yuan 800 a kowace shekara ba, an shigar da su cikin sunayen mutanen da suka samun tabbacin ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka, kuma an ba da babban taimako ga jama'a mafi talauci wajen likitanci, yawan kudin da suka samu wajen inshorar rasa aikin yi ya kai matsayi na farko na duk kasar Sin. Ban da wannan kuma an fara aikin gina gidajen kwana masu araha, sabo da haka jama'a masu yaki da talauci da ma'aikatan hukuma za su iya samun sharuda masu kyau wajen gidajen kwanansu.

---- A ran 22 ga watan Nuwamba a nan birnin Beijing, an yi taron duk kasa na 7 na kara wa juna sani kan ilmin kabilar Yi ta kasar Sin, kwararru da masanan ilmin kabilar Yi fiye da 150 da suka zo daga wurare daban-daban sun halarci taron.

Muhimmin take na wannan taro shi ne "raya zaman al'umma mai jituwa a shiyyar kabilar Yi da sa kaimi ga ci gaban al'adun kabilar", a gun taron masana mahalartan taron za su tattauna wannan batu kuma za su yi shawarwari kan yadda za a gaji kyakkyawan al'adun gargajiya na kabilar Yi ta kasar Sin, da sa kaimi ga ci gaban ilmin kabilar ta hanyar hadin gwiwa, da sauran jerin batutuwan da suka shafi matsalar samun bunkasuwa da wadata na kabilar Yi wajan zaman al'umma da tattalin arziki da al'adu.

Kabilar Yi tana daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin, yawan mutane 'yan kabilar ya kai fiye da miliyan 7 da dubu 760, wadanda suke zama a lardunan Yunnan da Sichuan da Guizhou da Guangxi da ke kudu maso yammadin kasar Sin.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet mai ikonm tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta rubanya kokari don bunkasa masa'antu masu sigar musamman na faffadan tsauni bisa manufar biyan bukatun kasuwannin kuma bisa matsayi mai rinjaye wajen albarkatun kasa, sabo da haka an samun babbar nasara wajen bunkasa tattalin arzikin masana'antu.