Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-07 16:07:02    
Yaki da ciwon sida a duniya

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Rasheed Isyaku, mazaunin birnin Zaria da ke jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. Malam Rasheed Isyaku ya rubuto mana wasika a kwanan baya da ke cewa, ranar 1 ga watan Disamba rana ce ta yaki da ciwon sida a duniya, shin yanzu mutane nawa ke fama da ciwon a duniya, kuma nawa ne a kasar Sin? Bayan haka, shin wadanne matakai ne gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar?

Masu karatu, cutar sida cuta ce mai yaduwa, wadda ke iya lalata tsarin garkuwa na jikin dan Adam, har ma ya sa ya rasa karfin garkuwar cututtuka iri iri. Muhimman hanyoyin yaduwar cutar sun hada da jini da gado daga mahaifiya zuwa jariri da kuma hanyar jima'i.

Tun bayan da manazarta na Amurka suka gano mai ciwon sida na farko a duniya a shekarar 1981, sai cutar ta yi ta yaduwa a duk fadin duniya cikin sauri, har ma ta zama abin da ke daukar hankulan jama'a sosai. A cikin shekaru da dama da suka wuce, ko da yake gamayyar kasa da kasa sun yi namijin kokari wajen yaki da cutar, har ma an sami cigaba, amma duk da haka, ba a samu shawo kan yaduwar cutar a duniya kamar yadda ya kamata ba. Bisa rahoton da hukumar kula da ciwon sida ta duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya suka hada kai suka bayar a ranar 20 ga watan da ya wuce dangane da ciwon sida a duniya a shekarar 2007, an ce, yanzu a duk fadin duniya, akwai mutane sama da miliyan 33 da ke dauke kwayoyin cutar sida.

Don kara fadakar da jama'a a kan illar ciwon sida, a shekarar 1988, kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta tsai da ranar 1 ga watan Disamba na kowace shekara a matsayin ranar yaki da ciwon sida ta duniya, don yin kira ga kasashe daban daban na duniya da su gudanar da bukukuwa daban daban a ran nan, ta yadda za a fadakar da jama'a a kan cutar.

A nan kasar Sin, bisa hadadden rahoton kimanta aikin yaki da ciwon sida a kasar Sin na shekarar 2007 da aka bayar kwanan baya a birnin Beijing, an ce, yanzu akwai masu dauke da kwayoyin cutar sida da yawansu ya kai kimanin dubu 700 a kasar Sin, kuma daga cikinsu, dubu 85 sun kasance masu ciwon sida. Ban da wannan, yawan sabbin masu dauke da kwayoyin cutar da aka gano a shekarar 2007 ya kai kimanin dubu 50, wato cutar ta sami sassaucin yaduwa bisa sabbin masu dauke da cutar dubu 70 da aka gano a shekarar 2005.

A hakika, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai a kan yaki da ciwon sida, tun daga shekarar 2006, kasar Sin ta kaddamar da ka'idojin yaki da ciwon sida, wanda ya shimfida harsashi ga aikin yaki da ciwon sida a fannin doka. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin cika alkawarin da ta dauka, kuma hukumomi na matakai daban daban sun kara zuba kudaden jari a fannin yaki da ciwon sida, har ma kudaden da gwamnatin kasar Sin ta ware musamman domin yaki da ciwon sida sun karu daga miliyan 850 a shekarar 2006 zuwa miliyan 940 a shekarar 2007. bayan haka, an kuma karfafa aikin rigakafi da ilmantarwa a duk fadin kasar, kuma wuraren da ke iya samun maganin kwayoyin cutar sida ba tare da biyan kudi ba a kasar Sin sun kara fadada. Har ila yau kuma, kungiyoyin al'umma da kamfanoni na kasar Sin suna ta kara sa hannu cikin aikin yaki da ciwon sida, kuma suna ta kara taka muhimmiyar rawa.

Amma duk da haka, hadadden rahoton kimanta aikin yaki da ciwon sida a kasar Sin ya kuma nuna kalubalen da ke gaban kasar Sin a fannin yaki da cutar, ciki har da kawar da bambancin da al'umma ke nuna wa mau dauke da kwayoyin cutar sida da kara raya masu yaki da cutar da dai sauransu. A game da wannan dai, ministan kiwon lafiya na kasar Sin, Dr.Chen Zhu ya bayyana cewa, kalubalen da kuma shawarwarin da aka gabatar a cikin rahoton za su iya ba da jagoranci ga kasar Sin wajen yaki da cutar.(Lubabatu)