Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-07 15:42:33    
Jihar Ningxia tana yaki da kwararowar hamada

cri

Gundumar Yanchi tana gabashin jihar Ningxia, kuma tana bakin hamadar Mu Us. Kuma sabo da illar da halittu da dan Adam suka yi a da, kwararowar hamada a gundumar tana ta tsananta.Kamar yadda mazaunan wurin su kan ce, ko a lokacin baraza, ko a lokacin hunturu, idan an yi iska, to za a samu rairayi a ko ina, haka kuma tudun rairayi ya fi dakuna tsayi.

Kwararowar hamada mai tsanani ta kawo cikas sosai ga bunkasuwar tattalin arziki na gundumar Yanchi, haka kuma wannan shi ne dalili mafi muhimmanci da ya sanya fararen hula na wurin su fama da talauci. Domin kyautata wannan mumunan halin da ake ciki kwata kwata, gwamnatin gundumar ta gabatar da wani ra'ayi, wato fama da kwararowar hamada domin samun bunkasuwa.

Gundumar Yanchi tana dukufa kan hadin gwiwa tare da kasa da kasa, kuma daya bayan daya ne ta samun kudaden kyauta da kasashen Japan da Jamus suka samar wajen dasa biushiyoyi. Liu Weize, mataimakin shugaban hukumar kula da bishiyoyi ta gundumar Yanchi ya bayyana cewa, ba kawai kasashen waje sun samar da kudade gare mu ba, har ma sun ba mu fasahohi da sakamako mai kyau wajen fama da kwararowawr hamada.

Yanzu bisa bayanin da tauraron dan Adam ya bayar, an ce, an riga an kau da kusan dukkan tudun hamada, ta haka an samu babban ci gaba wajen fama da kwararowar hamada.