Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-07 14:21:46    
Ana hangen nesa kan taron koli na biyu a tsakanin Turai da Afirka

cri

A ran 8 da 9 ga wata, shugabanni ko wakilai na kasashen mambobi 27 na kungiyar tarayyar Turai wato EU da na kasashe 53 na Afirka za su gana da juna a birnin Lisbon, babban birnin kasar Portugal, wadda ke rike da shugabancin EU a wannan karo, domin halartar taron koli na biyu da ke tsakanin kungiyar EU da Afirka. Lallai, za a shirya taron koli a tsakaninsu a karshe bayan da suka sha rikici da yawa. Wannan ya bayyana cewa, kungiyar EU tana aiwatar da manufofin hakika kan kasashen Afirka.

An shirya taron koli na farko a tsakanin Turai da Afirka ne a watan Afrilu na shekarar 2000 a birnin Alkahira, babban birnin kasar Massar. Bisa shirin da suka tsara, ya kamata su shirya taron koli na biyu a shekarar 2003 a birnin Lisbon, amma kungiyar EU ta ki gayyatar shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe, kasashen Afirka ba su gamsu da haka ba, a sakamakon haka, sau da yawa ne aka dakatar da shirya wannan taron koli na biyu a tsakaninsu. Bayan haka kuma, kasashen Portugal da Faransa da Spain da dai sauransu sun sa kaimi sosai domin shirya wannan taron koli, sa'an nan kuma aka tabbatar da lokacin da aka shirya taron koli na biyu. Bisa ajandarsa, za a tattauna kan zaman lafiya da aikin tsaro, da makaurata, da makamashi, da kuma sauyawar yanayi, haka kuma bangarorin biyu na Turai da Afirka za su zartas da yarjejeniyoyi biyu, wato 'manyan tsare tsare na hadin kan kungiyar EU da Afirka', da 'shirin daukan matakai daga shekarar 2008 zuwa ta 2010', ta yadda za su kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a tsakaninsu domin fuskantar karni na 21. Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, wannan taron koli ya sha bamban sosai idan aka kwatanta shi da halin da ake ciki a da.

A bangaren kasashen Afirka, suna kara hada hansu sosai domin karfafa kwarewarsu. A shekarar 2001, kasashen Afirka sun daddale wata yarjejeniya da kansu, wato shirin sabon kawancen raya Afirka, inda a karo na farko ne aka bayyana cewa, kasashen Afirka za su kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa tushen moriyar juna da zaman daidai wa daida da juna da kasashen yamma. Lallai, wannan ya sa kaimi sosai domin shirya taron koli na biyu da ke tsakaninsu da kungiyar EU.

A bangaren kungiyar EU kuma, a cikin wannan sabon hali, wato a 'yan shekarun baya, manyan kasashe daban daban sun fi mai da hankali sosai kan harkokin Afirka, ya zama wata babbar bukata domin kungiyar EU ta kara daga matsayin dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka. Kungiyar EU ta gano cewa, idan babu goyon baya da hadin kai daga kasashen Afirka, to, kasashen Turai ba za su iya cin nasara ba wajen yaki da ta'addanci, da tabbatar da samun makamashi yadda ya kamata, da daidaita matsalar sauyawar yanayi, da shawo kan yaduwar cututtuka da dai sauransu.

Ko da yake haka ne, ya kasance da rikici wajen raya sabuwar dangantaka da ke tsakanin kungiyar EU da kasashen Afirka, wata babbar matsalar ita ce, har yanzu dai, firayin ministan kasar Britaniya Gordon Brown yana tsayawa tsayin daka domin nuna dagiya da Robert Gabriel Mugabe wajen halartar wannan taron koli na biyu.

Kafofin watsa labarai suna ganin cewa, wannan taron koli na biyu a tsakanin kungiyar EU da Afirka, wanda aka shirya a birnin Lisbon, yana da muhimmiyar ma'ana, domin tabbatar da makomar dangantakar da ke tsakaninsu. Zaman daidai wa daida da amincewar juna, ba ma wata maganar banza ba, zai bukaci kungiyar EU da kasashen Afirka musamman kungiyar EU da su aiwatar da manufofin hakika.(Danladi)