Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-06 15:49:50    
Beijing zai horar da masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympics da fasahar duniya

cri

A ran 5 ga wata a birnin Beijing, an kaddamar da manyan aikace aikacen makon cudanya a tsakanin kasa da kasa dangane da masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing. A cikin kwanaki da dama masu zuwa, jami'ai da kwararru da suka zo daga kungiyoyin masu aikin sa kai na kasashe da yankuna 12 kamar Sin da Amurka da Australiya da Japan, za su more kyakkyawan sakamako da fasahohinsu tare da masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Bisa labarin da muka samu, an ce, wannan ya zama wani babban horo da aka yi wa masu aikin sa kai, kafin gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. Masu karbar horo sun hada da manajoji masu aikin sa kai da ke filaye da dakunan gasar wasannin Olympics, da kusoshin masu aikin sa kai, da masu aikin sa kai dalibai da suke karatu a jami'o'i da dai sauransu.(Danladi)