Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-05 20:23:03    
Shakar hayakin taba tana iya yin illa ga lafiyar dan Adam da kuma dabbobin gida

cri

Manazarta na kasar Amurka sun buga wani rahoto kan mujallar ilmin cutar hakora a watan Afril na shekarar da muke ciki, cewa sakamakon gwajin dabbobi ya bayyana cewa, shakar hayakin taba yana iya yin illa ga lafiyar baki, wato mai yiyuwa ne zai haddasa lalacewar wani sinadari kamar kashi da ke kan hakora game da mutanen da suke fama da cutar hakora.

A cikin gwajin da manazarta suka yi, da farko sun sa beraye sun kamu da cutar hakora. Daga baya kuma sun kasa wadannan beraya cikin rukunoni uku. Beraye na rukuni na farko suna zama a cikin muhallin da babu hayakin taba, na rukuni na biyu kuma suna zama a cikin muhallin da ke da hayakin taba kadan har kwanaki 30, yayin da na rukuni na uku suke zama a cikin muhallin da ke cike da hayakin taba har kwanaki 30.

Sakamakon gwajin ya nuna cewa, muddin berayen suka kasance a cikin muhallin da ke da hayakin taba, ko kuma sun shaki hayakin taba kadan ko da yawa, sun fi saukin samun lalacewar sinadari kamar kashi da ke kan hakoransu idan an kwatanta su da wadanda suka yi zama a cikin muhallin da babu hayakin. Kuma manazarta sun yi bayanin cewa, lalacewar sinadarin kashi shi sanadi ne mafi muhimmanci da ke haddasa zubewar hakora ga mutanen da suke fama da cutar hakora.

Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, kafin wannan, an riga an shaida cewa, ya kasance da dangantakar da ke tsakanin shan taba da cutar hakora, amma gwajin da suka yi ya bayyana cewa, shakar hayakin taba shi ma yana iya yin illa ga lafiyar baki.

Preston Miller, shugaban kungiyar kula da cutar hakora ta kasar Amurka ya bayyana cewa, ta wannan gwaji, mutane sun iya fahimtar cewa, shakar hayakin taba yana da illa sosai. Idan ana son kiyaye hanyar zaman rayuwa lami lafiya kamar yadda ya kamata, dole ne a bar wuraren da ke cike da hayakin taba da yawa. Bugu da kari kuma Mr. Miller ya ce, an riga an fara aiwatar da umurnin hana shan taba a wuraren jama'a kamar dakunan cin abinci da dai sauransu a wasu biranen kasar Amurka, kuma kungiyar kula da cutar hakora ta Amurka ta nuna amincewa sosai kan wannan batu. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba kawai mutane suna iya cin abinci cikin farin ciki ba, har ma za a ba da taimako wajen kiyaye lafiyar bakunansu.

Ya kamata masu shan taba su mai da hankali kan cewa, ba kawai shakar hayakin taba zai iya yin illa ga lafiyar sauran mutane ba, har ma zai iya yin illa ga lafiyar dabbobin gida nasu. Binciken da kasar Amurka ta gudanar a 'yan kwanakin nan da suka gabata a fannin ilmin likitanci na dabbobi ya tabbatar da cewa, game da dabbobin gida kamar kare da kyanwa, yiyuwar kamuwa da cutar sankara za ta karu sakamakon shakar hayakin taba.

Wata kungiyar nazari ta kwalejin koyon ilmin likitanci na dabbobi na Taft na kasar Amurka ta gano cewa, yawan kwayoyin sankara da ke cikin bakunan kyanwoyin da su kan shaki hayakin taba ya fi yawa idan an kwatanta su da wadanda suke da zama a cikin gidajen da ba a shan taba a ciki ba. Masu ilmin likitanci na dabbobi sun bayyana cewa, kyanwoyi sun fi saukin samun illar da shakar hayakin taba ya yi musu, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da su kan lashi gashinsu, ta haka sinadarin haddasa sankara na taba da ke cikin iska zai shiga bakunansu.

Bugu da kari kuma nazarin da jami'ar jihar Clolrado ta Amurka ta yi ya gano cewa, karnukan da su kan shaki hayakin taba sun fi saukin kamuwa da sankarar hanci. Kuma game da wadanda suka fama da sankarar, su kan mutu a cikin shekara guda.

Ban da wannan kuma nazarin ya gano cewa, sabo da abubuwa masu gurbata muhalli da ke cikin iska sun fi saukin lalata tsarin numfashi na tsauntsaye, shi ya sa game da wadanda su kan shaki hayakin taba, sun fi saukin kamu wa da sankarar huhu.