Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-05 20:07:17    
Jihar Ningxia tana sanya himma ga adana abubuwan tarihi da al'adu

cri

Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin tana daya daga cikin jihohi 5 na kananan kabilu masu aiwatar da harkokinsu na kansu na kasar Sin. Wajen raya tattalin arziki, jihar Ningxia ba ta kai matsayin sauran lardunan da ke bakin teku na gabashin kasar Sin ba, amma, tana da wadatattun abubuwan tarihi na al'adun gargajiyar kasar Sin. Kwanan baya, karo na farko ne jihar Ningxia ta sanar da sunayen abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba wadanda suke kunshe da nagartattun abubuwan tarihi na gargajiyar kasar Sin da yawansu ya kai 31.

Jihar Ningxia tana bakin rawayen Kogi wanda ya soma haifar da al'adun kasar Sin, kuma wuri ne mafi girma da 'Yan kabilar Hui suke zama a cunkushe a kasar Sin. A karni na 11, an taba kafa daular Xixia a wurin, a wancan zamani, an dinke wasu yankunan da ke arewa maso yammacin kasar Sin gu daya, inda aka samu halayen musamman na kabilu da yawa. Ya zuwa yanzu, a jihar Ninxia, ba ma kawai da akwai abubuwan tarihi na al'adun Xixia ba, hatta ma da akwai al'adun da ke da halayen musamman na kabilu daban daban na kasar Sin, alal misali, da akwai wakokin gargajiyar yankunan arewa maso yammacin kasar Sin tamkar wakar da ke da salon irin "Huaer" tare da al'adar Kabilar Hui da kayayyakin kida da tufaffin gargajiyar kabilar Hui da fasahar yanka takardu da ake yi da almakashi da sauransu, daga ciki, yawancinsu an riga an mayar da su bisa matsayin abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na jihar Ningxia. Wani direktan cibiyar kiyaye abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na jihar Ningxia Mr Jin Zongwei ya bayyana yadda jihar ta zabi abubuwan tarihi na al'adu don su zama abubuwan tarihi na al'adu na jihar, Mr Jin Zongwei ya bayyana cewa, da farko, da akwai ma'aunin da za a iya aiwatar da shi ba tare da katsewa ba a nan gaba. A wani daban kuma, zai ba da tasiri ga zaman rayuwar jama'a , sa'anan kuma, za a iya aiwatar da shi don yin gadon abubuwan tarihi na al'adu. A jihar Ningxia, babbar kabila ita ce kabilar Hui, za mu mai da hankali ga yin bincike kan abubuwan tarihi na al'adu dangane da aikin kawo albarka da zaman rayuwa na kabilar Hui da yi musu rajista.

Mr Jin Zongwei ya bayyana cewa, abubuwan tarihi na al'adu na jihar Ningxia suna kunshe da manyan fannoni 7 tare da ire-irensu dari da mutane da suke yin gadonsu dubu 150. Rukunin farko na abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na jihar suna hada da zane-zanen gargajiya da fasahar yanka takardu da aka yi da almakashi da fasahar yin ado ne ta hanyar dinki da sassaka tubali da yin mutum mutumi ta hanyar yin amfani da yambu da al'adar gargajiya tamkar yadda ake yi sallar layya da sauransu. An bayyana cewa, don kiyaye da yin gado da fasahar gargajiya wajen yin zane-zane da sauransu, an kafa kauyukan yin kayayyakin fasaha tamkar su kauyukan yin ado ta hayar dinki da na yanka takardu da aka yi da almakashi da sauran kauyukan yin kayayyakin fasaha. Wadannan kayayyaki sun jawo sha'awar mutane sosai. Wata malama Wang Xilian ta bayyana cewa, ta hanyar taimakon da aka bayar, kuma ana kan gabatar wa sauran wurare kayayyakin da wadannan kauyukan suka yi , shi ya sa samari su ma suka soma son koyon fasahar, suka kara fahimtar muhimmancin wadannan abubuwa, saboda haka, aka kara sa kaimi ga raya tattalin arziki.

Don kiyaye abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba, jihar Ningxia ta tsara ka'idojin jihar na kiaye fasahar yin zane-zanen gargajiya da sauransu a shekaru 90 na karnin da ya gabata, a shekarar 2005 musamman ne aka kafa cibiyar kiyaye abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba, a shekarar 2006, aka soma aiwatar da ka'idojin kiyaye abubuwan tarihi na al'adu na jihar, a shirye ta ke jihar Ninxia za ta kammala aikin bincike abubuwan tarihi na al'adu a duk fadin jihar da kuma yi musu rajista, ya zuwa shekarar 2020, za a kiyaye abubuwan tarihi na al'adu na jihar Ningxia daga dukkan fannoni.(Halima)