Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-05 15:40:15    
An rufe taron shugabanni na kwamitin hadin kan kasashen Larabawa na gulf a karo na 28

cri
Ran 4 ga wata, an rufe taron shugabanni na kwamitin hadin kan kasashen Larabawa na tekun gulf a karo na 28 wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a Doha, babban birnin kasar Qatar. Taron ya bayar da "sanarwar Doha" da sanarwar karshe, kuma ya sami ra'ayi daya a kan harkokin tattalin arzikin gulf da zaman lafiyar yanki.

A gun bikin rufe taron, Abdul Rahman al-Attiya, babban sakataren kwamitin ya sanar da cewa, wannan taron koli ya yanke shawara a kan fara aiki da kasuwar tarayyar gulf a shekarar badi. Ya ce, "hukumar koli ta kwamitin hadin kan kasashen Larabawa na tekun gulf ta sanar da cewa, tun daga ran 1 ga wtan Janairu na sabuwar shekara, za a fara aiki da kasuwar tarayyar gulf."

A gun taron shugabannin a karo na 23 da aka yi a shekarar 2002, kwamitin ya gabatar da cewa, za a kafa kasuwar tarayyar gulf. Makasudin kafuwarta shi ne domin ba da tabbaci ga nuna daidaici ga 'yan kasashen kwamiti da ke zaune a duk kasashensu a fannonin zaman rayuwa da aikin yi da zuba jari da yin ciniki da samun magani da ilmi da sauransu. Bisa jadawalin lokacin da aka tsara a wannan lokaci, za a kafa kasuwar tarayyar gulf kafin karshen shekarar nan. Bisa kokarin da aka yi ta yi a cikin shekaru 5, kasashen kwamitin sun riga sun sami ra'ayi daya a kan kasuwar da za su kafa a fannoni daban daban. Da al Attiya ya tabo magana a kan manufar kasuwar, sai ya ce, za a kafa kasuwar ne domin jama'ar kasashen gulf daban daban za su ci gajiyar tattalin arzikin gulf, da kara daga matsayin kasashen kwamiti a cikin tsarin tattalin arzikin duniya.

Wani abu mai muhimmanci a taron shugabannin shi ne Mahmoud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa. Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, kasashen kwamitin suna fatan za su inganta huldar da ke tsakaninsu da kasar Iran wadda kasa ce mai muhimmanci da ke makwabtaka da su.

A gun wannan taron shugabanni, kasashen gulf sun dora muhimmanci sosai ga kasar Sin wadda ke kara daga matsayinta a fannin harkokin siyasa da tattalin arziki a duniya. Da Al-Attiya ya amsa tambayar da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya yi masa cewa, kwamitinsa zai sake yin shawarwari a tsakaninsa da kasar Sin a kan kafa yankin cinikayya maras shinge kafin karshen shekarar nan. Ya ce, "kafa yankin cinikayya marar shinge a tsakanin kasashen kwamitin tarayyar kasashen Larabawa na gulf da kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga tattalin arziki da ciniki na bangarorin biyu. Yanzu, an riga an sami kyakkyawan sakamako wajen yin shawarwari kan kafa yankin cinikayya marar shinge a tsakanin bangarorin biyu. Wakilansu mahalartan shawarwarin sun sami babban ci gaba a fannonin hidimna da hajjoji da kuma sauran fannoni masu muhimmanci. Kafin karshen shekarar nan, za mu sake yin shawarwari tare da kasar Sin. Zuwan wancan lokaci, za a sami hakikanin ci gaba wajen yin shawarwarin."

Ban da wadannan kuma wannan taron shugabanni na kwamitin ya sami ra'ayi daya a kan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da yawa. Da Sheikh Hamad Bin Khalifa Al Thani, shugaban kasar Qatar ya tabo magana a kan sakamakon da aka samu a gun taron, sai ya bayyana cewa, "kiran wannan taron shugabanni tare da nasara ya danganta da kokarin da kasashen kwamitin suka yi ba tare da kasala ba, kuma zai kara bunkasa kasashen gulf da tabbatar da zaman karkonsu da kuma kara dankon aminci da ke tsakaninsu. Za mu ci gaba da yin kokari don kara samun kyakkyawar makomar jama'ar kasashen gulf, da kara inganta huldar aminci da ke tsakanin kasashen gulf daban daban." (Halilu)