Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-05 08:58:10    
An yi gasar keken hanyar mota ta duniya ta shekarar 2007 a tsibirin Hainan na kasar Sin

cri

Masu sauraro,daga ran 3 zuwa ran 10 ga watan Nuwamba na shekarar bana,an yi gasar keken hanyar mota ta duniya ta shekarar 2007 a jihar Hainan,wato jiha mai nisa a kudancin kasar Sin,wannan shi ne a karo na biyu da jihar Hainan ta dauki bakuncin shirya gasar nan,bayan kokarin da aka yi,gasar bana ta sami cikakkiyar nasara.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan. 

Daga ran 3 zuwa ran 10 ga watan Nuwamba na bana,an yi gasar keken hanyar mota ta duniya ta shekarar 2007 a jihar Hainan dake kudancin kasar Sin.Kamar yadda kuka sani,a wannan lokaci,yawancin wuraren kasar Sin sun riga sun shiga yanayin sanyi,amma a jihar Hainan,ko ina ana iya ganin furanni iri daban daban,musamman a tsibirin Hainan,ana iya jin nishadi a nan sosai da sosai,ban da wannan kuma,Tsawon bakin teku na tsibirin ya kai fiye da kilomita 1580.`Yan wasa sun fara gasa ne daga birnin Sanya wanda shi ne wuri mai nesa a kudancin tsibirin Hainan,daga baya kuma za su gudu kan keke a kewayen tsibirin,a karshen gasar,za su sake komawa wurin.A kan hanya,za su ketare birane da gundumomi 15.`Yan wasa sun ji farin ciki kwarai da gaske saboda yin gasa kan hanya tsakanin duwatsu da teku.`Dan wasa daga kungiyar Marco Polo ta kasar Holand Thijs Zonneveld ya bayyana cewa,  `Wannan shi ne a karo na farko da na zo Hainan domin shiga gasa,na ga ruwan teku mai launin shudi,kuma na ga itace mai launin kore,na ji dadi kamar ina cikin aljanna.Za mu yi iyakacin kokari domin samun sakamako mai gamsarwa.`

Kazalika,alkalan wasa da `yan wasa su ma suna gamsar da ingancin hanyar mota ta jihar Hainan,shi ya sa kawancen wasan keke na duniya ya daga ajin gasa daga 2.2 zuwa 2.1,a sanadiyar haka,yawan kungiyoyin `yan wasa da suka shiga gasar bana sun kara karuwa kuma matsayinsu shi ma ya dada daguwa a bayyane.Don kara kyautata aikin karbar `yan wasa da alkalan wasa da `yan jarida da sauran ma`aikatan da abin ya shafa da yawansu suka kai fiye da 560,karamar gwamnatin jihar Hainan ta daddale yarjejeniya da dukkan manyan masaukin baki wadanda suka kai matsayin taurari uku ko fiye domin samar da aikin hidima mai kyau.Alkalin wasa na matsayin A na kawancen wasan keke na duniya da kuma mataimakin babban manajan kamfanin shirya wannan gasa Qiu Jijin ya ce:  `Sharuddan manyan masaukin baki suna da kyau kwarai da gaske,abincin da ake samar mana suna da dadin ci sosai da sosai,muna jin dadi.`

Kamar yadda kuka sani,`yan wasan sana`a sun hau keke da saurin gaske,har saurinsu ya kai kilomita 80 a kowace awa,shi ya sa aikin tsaron lafiyar jikin mutane yake da muhimmanci,wato idan mutum ko mota sun shiga hanyar gasa,to,hadari zai faru.A shekarar bana,a gun gasar keken da aka yi a tsibirin Hainan,gaba daya hukumomin `yan sanda na matsayi daban daban na jihar Hainan sun tura `yan sanda da yawansu ya kai 10500 tare da motocin `yan sanda 1300.A kullum ana rufe babbar hanyar mota kafin a fara gasa cikin lokaci,wato a hana mutum ko mota su shiga,domin gudanar da gasa lami lafiya.Malam Qiu Jijin ya ce:  `Kawancen wasan keke na duniya ya gamsu da aikin tsaro na wannan gasa sosai da sosai,sanin kowa ne,wasan keke yana da nasaba da sufuri,halin sufuri na wannan gasa ya yi kyau fiye da kima,har ma ana iya cewa,ya fi na sauran gasa da aka shirya a kasashen Turai.Wasu alkalan wasa da suka zo daga kasashen Turai su ma sun ji mamaki saboda irin wannan tsarin sufurin da aka kiyaye a gun gasar.

A cikin kwanaki 8 da suka shige,wato daga ran 3 zuwa ran 10 ga watan Nuwamba na shekarar 2007,gaba daya `yan wasa da alkalan wasa da `yan jarida sun darajanta ni`imtaccen wuri da yanayi mai kyau da hanya mai inganci da aikin karbar baki da aikin tsaro na jihar Hainan sosai.Ko shakka babu,gasar wasan keken hanyar mota ta duniya ta kewayen tsibirin Hainan ta riga ta dosa gaba a kan hanyar shirya gasa ta matsayin gaba a duniya.?Jamila Zhou)