Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-05 08:56:23    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (28/11-04/12)

cri

Daga ran 10 ga wata ne,kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing zai fara aikin sayar da tikitin kallon bikin bude da rufe gasar wasannin Olympic ta makasassu ta Beijing ta shekarar 2008 da kuma tikitin kallon gasar da za a shirya a cikin yankin kasar Sin,dukannin mutane wadanda ke mallakar gidajen kwana da takardar shaida mai amfani a cikin yankin jamhuryar jama`ar kasar Sin suna iya samun iznin sayen tikitin.Gaba daya yawan tikitin kallon bikin bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing wanda za a sayar da su a fili a cikin yankin kasar Sin ya kai dubu 21,yawan tikitin kallon bikin rufe gasar kuma ya kai dubu 26.Za a sayar da tikitin bisa adalci.Idan ana so a sayi tikitin,to,daga ran 10 zuwa ran 30 ga wannan wata sai ka shiga tashar internet ta gwamnatin kasar Sin wadda ke sayar da tikitin gasar wasannin Olympic ta Beijing,ko ana iya zuwa ofisoshin sayar da tikiti guda dubu 1 na bankin kasar Sin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya nada domin gabatar da takardar rokon sayen tikitin.

Ran 30 ga watan jiya,kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya sanar da manufar sayar da tikitin kallon gasar wasannin Olympic ta Beijing a cikin yankin kasar Sin ta mataki na biyu a birnin Beijing,inda aka tanada cewa,bisa mataki na biyu,za a fara karben takardar bukatar sayen tikitin daga ran 10 ga wata,kuma za a kawo karshen aikin a ran 30 ga wata,idan yawan tikitin da za a bukatar sayensu ya zarce yawan tikitin da za a sayar da su,to,na`urar kwakkwalwa za ta yi zabe.Ban da wannan kuma,kwamitin shirya gasar wasannin Olympic shi ma ya tanadi cewa,yawan tikitin da kowanen mutum zai saye ba zai wuce takwas ba.

Ran 3 ga wata da asuba,bisa agogon Beijing,aka kawo karshen gasar cin kofin duniya ta shekarar 2008 ta wasan kankara a kasar Italiya,kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya biyu.A gun zagaye na karshe na gasar mata ta mita dari 5,`yar wasa daga kasar Sin Wang Meng ta samu zama ta farko bisa dakika 44 da motsi,wata `yar wasa daban daga kasar Sin Fu Tianyu ta samu zama ta biyu.A cikin zagaye na karshe na gasar wasan kankara ta ba da sanda ta mata ta mita dubu 3,kungiyar kasar Sin ta zama zakara bisa minti 4 da dakika 17 da motsi.

Ran 3 ga wata da asuba,agogon Beijing,aka fara gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon hannu ta mata ta shekarar 2007 a kasar Faransa,a cikin zagaye na farko na rukunin D,kungiyar kasar Romaniya ta lashe kungiyar kasar Sin,gaba daya kungiyoyi 24 ne za su shiga gasar nan,kuma aka rabe su bisa rukunoni 6.?Jamila Zhou)