Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 20:17:27    
Kasar Sin tana kokarin zama wata kasa da ke da kyakkywan muhalli a shekarar 2020

cri

Saurari

A ran 4 ga wata a gun wani taron manema labaru da aka yi a birnin Beijing, Mr. Zhu Lieke, mataimakin shugaban hukumar gandun daji ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yadda za a kafa wani muhalli mai daukar sauti da kiyaye muhalli. Kuma tana kokarin zama wata kasar da ke da kyakkyawan muhalli a shekarar 2020. Mr. Zhu ya ce, "kasar Sin za ta kara mai da hankali kan raya muhalli mai daukar sauti, musamman za ta kara shuka itatuwa da kyautata halin da ake ciki ta fuskar yankunan kasa. Kuma za ta ci gaba da sa kaimi kan mutanen da suka dosa itatuwa bisa nauyin tilas da ke bisa wuyansu. A waje daya kuma, za a kara kiyaye gandun daji da mayar da wasu gonaki da su zama gandun daji da kuma shimfida itatuwan maganin kwararowar hamada a yankunan birnin Beijing da na Tianjin da sauran yankuna 3 da ke arewacin kasar Sin da na arewa maso yammacin kasar da kuma na arewa maso gabashin kasar da dai makamatansu."

Mr. Zhu Lieke ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta kara daukar matakai iri daban-dabam domin kara kiyaye gandun daji da kyautata ingancin gandun daji, kuma za a kara kiyaye namun daji da tabbatar da ganin halittu iri daban-daban sun yi zama tare cikin lumana.

A cikin shekaru da yawa da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen gina muhalli mai daukar sauti da kiyaye muhalli da namun daji. Yanzu, yawan gandun daji da kasar Sin take da su ya kai hekta miliyan 175, wato ke nan ya kai kashi 18.21 cikin kashi dari bisa na dukkan yawan fadin kasar. Amma, a shekarar 1949, wato shekara ce da aka kafa Jamhuriyar Jam'ar Sin, wannan adadi ya kai kashi 8.6 cikin kashi dari. Yawan gandun daji da aka shuka yana matsayin farko a duk duniya.

An bayyana cewa, muhimman buri da nauyin kafa wani kyakkyawan muhalli da ke bisa wuyan gwamnatin kasar Sin su ne, ya zuwa shekarar 2020, fadin gandun daji da kasar Sin za ta shimfida zai kai fiye da kashi 23 cikin kashi dari bisa na duk fadin kasar Sin. Yawan gandunan daji da albarkatu iri iri da ke cikinsu zai kai kimanin 2300, fadinsu zai kai kashi 14.5 cikin kashi dari bisa na fadin duk kasar Sin. A waje daya kuma, yawan muhimman namun daji da sauran halittu iri iri da za a kiyaye su zai kai kashi 95 cikin kashi dari bisa na dukkan namun daji da sauran halittu iri iri da ya kamata a kiyaye su.

Lokacin da yake tabo magana kan cigaban da kasar Sin samu wajen hana gonakin da su zama hamada, Zhu Lieke ya ce, bayan da kasar Sin ta yi shekaru 10 tana kyautata irin wadannan gonaki, fadin wuraren hamada yana raguwa. Alal misali, a karshen karnin da ya gabata, fadin gonakin da hamada ke lalatawa a kowace shekara ya kai murabba'in kilomita dubu 3, amma tun daga farkon karnin da muke ciki, fadin gonakin da hamada ke lalatawa ya ragu da murabba'in kilomita dubu 1 da dari 2 a kowace shekara. A watan Janairu na shekara mai zuwa, majalisar dinkin duniya za ta shirya wani taro a nan kasar Sin domin yada fasahohin yaki da kwararowar hamada a gonaki da kasar Sin ta samu.

Mr. Zhu Lieke ya bayyana cewa, a nan gaba, lokacin da kasar Sin take kafa kyakkyawan muhalli, za ta ci gaba da mai da hankali kan batun yaki da kwararowar hamada a gonaki. Mr. Zhu ya ce, "gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan wannan batu sosai. A farkon shekarar da muke ciki, hukumar gandun daji ta kasar Sin ta wakilci majalisar gudanarwa ta kasar ta kulla yarjejeniyoyin tabbatar da nauyin tilas da gwamnatocin muhimman larduna 12 domin hana kwararowar hamada a gonaki, wato a bayyane ne ta tabbatar wa wadannan larduna burin da dole ne za su cimma. A waje daya kuma, kasar Sin ta riga ta tsara shirin hana gonaki da su zama wuraren hamada."